Babban Hafsan Tsaro na sojojin Najeriya Christopher Musa ya ce Sojoji ba za su yi Juyin Mulki na a Najeriya kamar yadda wasu ke fata cikin masu zanga-zanga.
Musa ya ƙara da cewa lallai rundunar soji za ta hukunta duk wanda aka kama yana daga Tutar kasar Rasha a Najeriya da sunan zanga-zanga.
Masu zanga-zanga a jihohin Kaduna, Kano, Filato da Abuja sun riƙa ɗaga tutar Rasha yayin da suka Zanga-zanga.Sai dai kuma CDS Musa ya ce sojoji ba za su saka ido su bari ana yi wa Najeriya irin wannan cin fuska ba.
Ya kara da cace yanzu haka suna nazartar abunda yake faruwa a Najeriya na tashe – tashen hankula da sunan zanga – zanga domin duba yiwuwar daukar matakin Soji akai duk da cewa ‘yan sanda suna iya bakin kokarinsu don tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Game da kiraye kiraye da masu zanga-zanga ke yi wai sojoji su yi juyin mulki, ya ce ba za su yi juyin mulki ba.
” Muna tare da Dimokuraɗiyya ɗari bisa ɗari kuma, za mu ci gaba da kare ta ɗari bisa ɗari. Ba bubwani soja da zai yi juyin.mulki a Najeriya yanzu. Kuma masu so su hargitsa mana kasa su kwana da shiri za mu bi su dul inda suke mu hukunta su.
Musa ya yi wannan jawabi ne yayin tattaunawa da ya yi da mabema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa ta musamman da suka yi.
Discussion about this post