Ministan Kula da Lafiya da Inganta Rayuwa, Muhammad Pate, ya bayyana cewa kashi 67 bisa 100 na ƙwararrun likitocin Najeriya duk sun gudu, sun koma aiki a Ingila.
Ya ce a Birtaniya ana rububin likitoci da jami’an kula da lafiya, da Nas-nas ‘yan Najeriya.
Pate ya ci gaba da cewa idan likitoci da nas-nas ‘yan Najeriya suka janye daga Birtaniya, to ƙasar za ta shiga gararin matsalar kiwon lafiya.
Da yake jawabi a Gidan Talabijin na a ranar Talata, Minista Pate ya ce Gwamnatin Bola Tinubu ta na bijiro da shirye-shiryen da za su magance hijirar da likitoci ke yi daga Najeriya zuwa ƙasashen waje.
A cikin watan Maris ma Pate ya ce likitocin da ke Najeriya ba su wuce 55,000, alhali kuwa yawan ‘yan Najeriya sun haura mutum miliyan 200.
Ya ce a cikin shekaru biyar likitoci 16,000 sun fice daga Najeriya, wasu kuma 17,000 an yi masu canjin wurin aiki.
“Ba za mu hana duk mai don ficewa zuwa wata ƙasa tafiya ba. Mun san idan ma sun tafi, ai wasu shigowa za su yi daga wasu wuraren.
“Za mu yi ƙoƙarin ganin mun gyara tsarin ta yadda masu ficewa za su yi daɗin aiki a cikin ƙasar nan, har su ji ba su ma so su fice daga Najeriya.” Inji Pate.
Discussion about this post