Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa a karon farko malejin tsadar rayuwa da na abinci ya sauka, saukar da tun da ya fara cillawa sama watanni 18 da suka gabata, bai gangaro ba sai a wannan karo.
Sai dai kuma wannan ƙididdiga ba ta jerin zubin carbin watanni ba ce, ƙididdiga ce ta lissafin shekara-shekara.
A lissafin watanni kuma watanni biyar kenan malejin na yin sama, bai sauka ba, sai wannan karo, inda ya yi saukar da talakawa da marasa galihu ba za su iya tantance barcin makaho ba.
Cikin watan Yuli malejin tsadar rayuwa ya ɗan sauko zuwa kashi 33.40 daga kashi 34.19 a watan Yuni.
Tun da 2024 ta shigo, duk wata sai malejin ya cilla sama, tun daga Janairu inda ya kai kashi 29.90.
Malejin tsadar abinci kuma tsadar rayuwa a watan Yuli 2024 ya dangwale 39.53, amma a Yulin 2023 ya na 26.98, lamarin da ya nuna an samu ƙarin kashi 12.55 a tsakanin Yuli 2023, zuwa Yuli 2024.
Tun da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya cire tallafin fetur aka afka cikin raɗaɗin tsadar rayuwa, lamarin da ya kai ‘yan Najeriya fitowa zanga-zangar kwanaki 10.
PREMIUM TIMES Hausa a tsakiyar Yuli ta buga labarin yadda malejin tsadar abinci ya dangwale kashi 40.87, yayin da burkin haƙurin ‘yan Najeriya ya tsinke daidai gangara.
Wannan gangara da ya kai ne har ‘yan Najeriya suka hasala, suka fita zanga-zangar da ta rikiɗe tarzoma a wasu garuruwa.
A lissafin na Yuli, Jadawalin tsadar rayuwa da raɗaɗin hauhawar farashin kayan abinci da kayan masarufi wanda Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar ranar Litinin ɗin nan, sun nuna cewa malejin tsadar kayan abinci ya dangwale zuwa kashi 40.87% bisa 100% a watan Yuni, 2024.
Hakan na nuni da cewa ya ƙaru da kashi 15.62% bisa 100% idan aka kwatanta da gejin sa na watan Yuni 2023, inda a lokacin yake daidai kashi 25.25% bisa 100%.
Haka kuma NBS ta ce malejin game-garin tsadar rayuwa ya haura zuwa kashi 34.19% bisa 100%.
Ƙididdigar ta NBS, wadda hukumar gwamnatin tarayya ce, tattabar da cewa tsawon watanni biyar kenan aka shafe duk wata kayan abinci da kayan masarufi na fuskantar tashin farashi.
Najeriya ce dai ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a Afrika, kuma ƙasa mafiya yawan jama’a a Afrika.
Sai dai kuma ‘yan ƙasar sun afka cikin masifar tsadar rayuwa tun daga ranar da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur, a ranar 29 ga Mayu, 2023 tun a wurin da aka rantsar da shi.
Tsadar rayuwa ta ƙara tsamari yayin da gwamnatin Najeriya ta yi sagegeduwar sakacin da darajar Naira ta karye a kasuwar canjin kuɗaɗen waje.
Duk da masifar tsadar rayuwa da ake fama a ƙasar, har yau ana kiki-kaka wajen kasa samun matsaya dangane da batun ƙarin mafi ƙanƙantar albashi, wanda fiye da shekara ɗaya ake ta tsallen-gada a kan sa.
Wannan sabuwar ƙididdiga ta NBS, ta zo yayin da ‘yan Najeriya ke ta kartar ƙasar furucin shirin fitowa su yi wa gwamnati zanga-zanga a ƙarshen watan Yuli.
Idan aka kwatanta malejin tsadar rayuwa na watan Yuni 2023, za a ga ya tsaya ne daidai kashi 22.79. Yanzu kuwa a Yuni 2024, ya dangwale zuwa kashi 33.95, inda cikin shekara ɗaya aka samu ƙarin gwauron tashi da kashi 11.40.
Discussion about this post