Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa maganar bacewar Fayilolin shari’arsa zance ce mara kangado da kuma rainin wayau a cikinsa.
Ganduje ta bakin kakakin sa Edwin Olofu, ya ce bacewar takardu masu mahimmanci irin wadannan, nuniya ce cewa gwamnatin jihar bata da kargo kuma ba za ta iya kula da mutanen jihar ba.
” A ce takardu masu mahimmanci irin haka a wuri mai mahimmanci a jihar a kasa tsare su, har wasu su kutsa su arce da su. Akwai lalaci, rashin iya aiki da kwarewa wajen sanin yadda za a gudanar da mulkin al’umma.”
” Abin ma yadda kasan wasan kwaikwayo, a ce wai da gwamnati a jiha, sannan wai wasu su dunguma cikin wuri irin Kotu mai mahimmanci su waske da takardu masu mahimmanci a jihar Kano, aiko ka san akwai wargi ciki. Babu wani mai hankali da tunani da zai yarda da wannan tatsuniyar da gwamnatin jihar ke shararawa.
Ganduje ya ce batun sace fayil din wani yunkuri ne na karkatar da bayanai kan fallasa wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar da aka yi a Kano da ya yi sanadiyyar dimbin asara da aka yi.
“Kowa ya sani gwamnan jihar Kabir Yusuf da bakin sa ya bayyana goyon bayansa ga wannan zanga-zanga kawai domin nuna adawa ga gwamnatin Tinubu, da akarshe ya yi sanadiyyar tarwatsa jihar.
Discussion about this post