Hukumar Kwastam dake aiki a tashar jiragen ruwa dake Apapa ta kama kwantena 12 danƙare da tramadol, magungunan da wa’adin aikin su ya kare da adduna 27,540.
Hukumar ta ce kudaden kayan da aka kama sun kai naira biliyan 1.8.
Shugaban hukumar Bashir Adeniyi ya sanar da haka ranar Alhamis a jihar Legas.
Adesuyi ya ce magungunan da suka kama an shigo da su kasar nan ba tare da tattance su ba sannan da dama daga cikin kwayoyin basa dauke da lambar rajista na hukumar NAFDAC.
“Mun kama wasu kwantena saboda rashin bayyana abin dake cikin su wasu Kuma sun yi kokarin kauce wa biyan kudin haraji ne.
“Daya daga cikin kwantenonin da muka kama mai lamban kamar haka SEGU4339917 na dauke da magungunan da suka hada da baclofen tablets, metoprolol succinate, atenolol gloves, losartan potassium, hydrochlorothiazide, atorvastatin calcium, esomeprazole magnesium da diclofenac sodium topical gel da sauran su.
Ya ce da dama daga cikin magungunan da hukumar ta kama ba sa dauke da lambar rajista na hukumar NAFDAC.
Adeniyi ya ce wani kwantena da suka kama na dauke da kwayoyin Royal Tramadol hade da Analgesic, antiseptic da basa dauke da lambar rajista na NAFDAC.
“An samu adduna 15,540 da wukake 12,000 a cikin wani kwantena.
A ƙarshe ya jinjina kokarin da jami’an hukumar ke yi a Apapa, da sauran wurare, ya na mai cewa hukumar za ta ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da ganin an rika kama ma su shigowa da muggan kwayoyi irin haka.
Discussion about this post