Ya kamata duk mai ruwa da tsakj a kan Nijeriya, kama da shugabanni da hukumomin tsaro, su sani fa, mulkin dimokaradiyya ake, muna aiki ne da kundin tsarin mulki. Ita kanta gwamnatin ta al’ummah ce suka zabe ta. Ya kamata a bawa al’ummah damar walwala irin ta dimokaradiyya.
Ita Zanga Zanga fa, gushire ce wanda take karawa Dimokaradiyya armashi da inganci, duk yunkuri danne al’ummah akan hana su yin zanga zanga ta kowace fuska, yin zagon kasa ne ga dimokaradiyya.
Ko da a kasar USA da ake ga ita ce kan gaba a dimokaradiyya, ko a wannan makon sai da Yan kasar ta suka yi zanga zanga don zuwan Shugaban Kasar Israela Natanyahu.
Gaskiya abin takaici ne, a wannan lokacin da Yan Siyasa masu mulkin yau, da su suka fi kowa cin moriyar zanga zangar siyasa, tun zamanin sojoji da ma yanzu, musamman ma irin su Shugaba Tinubu, amma a yau suna kokarin hana wasu yin abin da doka da dimokaradiyya ta amince musu
A mulki irin na dimokaradiyya Saka bakin wannan hukunomi ba kawai tozarci ne ga dimokaradiyyar ba, koma baya ne ma ga wannan hukumomi da suke fama kalubale a aiyukan su.
Ina hukumomi irin na su Yansanda da Civil Defense, wanda sune su ke aiki kai tsaye cikin alummah?
A wanna lokaci da Yan kasarnan suke cikin tsananin masifar rashin tsaro, wanda wannan kalubale ne ga su sojojin wannan kasa da ma su jami’an tsaro na boye, na kasa kawo karshen Yan Ta’adda da Yan Fashin Dajj dama masu ikirarin raba wannan kasa, irin su IPOB, duk da makuden kudaden da ake sanya a wannan bigere, sai gashi sunbar taiki suna dukkan wani abu daban.
Duk da kasancewar ni ra’ayina a yanzu, shin duk sakon da a ke so a isar ga shugabanni a wannan zanga zanga, sakon ya kai ga kunnen su. Tunda Shugaban ya amsa cewar Yan Kasa suna shan wahala, kuma sun dauki aniyar gyarawa nan take. Kuma tayi rokon a hakura da wannan zanga zangar, da dukkan alamu cikin gwamnati ya duri ruwa.
Suma kansu, masu shirin zanga zangar ya kamata a yi hakuri a dau bartaye, domin sake bawa shi shugaba Tinubu lokaci don warware alkawuran da ya dauka.
Don kare martabar Nigeria da wannan hukumomin tsaro, da su maida hankali a kan aiyukansu na kare kasa.
Discussion about this post