Shugaban jami’ar Afe Babalola, dake Ado Ekiti, Afe Babalola ya nuna rashin jin dadin sa kan yadda gwamnatin Najeriya ta ke raba wa yan kasa tallafin abinci, cewa ya maida yan kasa mabarata, sun koma maroka kawai.
Babalola ya bayyana haka yayin da yake amsar bakuncin kungiyar (Prestige Sisters League) da suka kawo masa ziyarar ban girma a jami’arsa.
Ya ce wadanda ke zanga-zanga saboda tsananin yunwa da ake fama da shi na da damar yin haka domin kowa ya sani ana yunwa a kasa.
” Wadanda suka fito zanga-zangar nuna yunwa da ake fama da, suna da damar yin haka, domin tabbas ana yunwa a kasar nan. Kuma hakkin gwamnati ne ta duba korafinsu ta kuma magance su.
” Hakkin gwamnati ne ta samarwa mutane zaman lafiya da walwala, amma ba a samun haka yanzu a Najeriya. Kowa ya dawo kusa da inda yake ganin zai samu natsuwa da kwanciyar hankali, an kaurace wa gonaki saboda hare-haren yan bindiga.
Saboda gazawar gwamnati, shi yasa ake fama da tsananin yunwa a kasa Najeriya.
Discussion about this post