Ɗan Majalisar Tarayya Alhassan Ado-Doguwa, ya yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso da Ɗan Majalisar Tarayya, Abdulmumin Jibrin-Kofa, cewa su daina cusa wa Kanawa ƙiyayyar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC.
Doguwa, wanda shi ke wakiltar Ƙananan Hukumomin Tudun Wada da Doguwa, ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya aika wa PREMIUM TIMES.
Ya ce Kwankwaso wanda ya yi takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin NNPP a zaɓen 2023, an gan shi a wani guntun bidiyo ya na kwankwatsar APC da shugabannin ta.
A cikin sanarwar da Doguwa ya fitar, ya ce tilas fa sai jama’a sun yi haƙuri, su bai wa Shugaban Ƙasa lokaci ya saisaita ƙasar nan.
Ya yi kira ga Kwankwaso ya daina cusa wa mutane ƙiyayyar APC da gwamnatin APC.
“Idan za ku iya tunawa, jagoran NNPP Kwankwaso ya riƙa zagin dukkan shugabannin APC a cikin wani guntun bidiyo, a Jihar Kano. Ya kira mu ‘Banzaye da Hausa.
“Ina kira gare shi da ya daina cusa wa matasa ɗabi’ar ɗaukar doka a hannun su, ta hanyar yin munanan kalamai a cikin bainar jama’a, masu iya tunzira matasan ɗaukar doka a hannun su a jihar.”
‘Ni Ba Tsarar Ka Ba Ne, Tsarar Ubangidan Ka Ne A Majalisa’ – Raddin Doguwa Ga Jibrin’:
Doguwa wanda ya fara yin Majalisar Tarayya tare da Kwankwaso a Jamhuriya ta Uku, wadda Kwankwaso ya yi Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, ya yi fatali da shawarar da Jibrin-Doguwa ya ba shi, mai wakiltar Ƙiru da Bebeji, cewa ya daina cin zarafin Kwankwaso.
Ya ce Jibrin yaron sa ne a siyasa, amma Kwankwaso ne tsarar sa, domin sun fara yin majalisa tare daga 1991 zuwa 1992.
Ya ce Jibrin bai san tarihin siyasa ba, da ya sani kuwa da zai san tarihin Doguwa ɗin tare da Kwankwaso.
“Idan Kwankwaso na so a riƙa ganin darajar sa da girman sa, to ya riƙa ganin darajar shugabannin APC da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.”
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Jibrin, inda ya ce Kwankwaso mutum ne mai son zaman lafiya, amma shi Doguwa ba wani abu ya ke nema ba sai neman suna kawai, shi ya sa ya damu da yawan kiran sunan Kwankwaso.
Ya ce Doguwa ya na yawan zagin Kwankwaso don tsammanin sa zai burge Tinubu ya ƙara samun shiga kusa da shi.”
Haka Jibrin ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar, mai sa hannun Hadimin Yaɗa Labarai, Sani Ibrahim-Paki.
Discussion about this post