Bayan shan tambayoyi da shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Jalal Arabi ya yi a makonni davsuka wuce, hukumar ICPC ita ma ta dira ofishin hukumar ranar Laraba.
Ga dukkan alamu dai hukumomin binciken harkallar kuɗaɗe musamman ga ma’aikatan gwamnati ba su gamsu da bayanan da shugaban hukumar Arabi ya rika bayarwa ba kan yadda ya kashe naira har biliya 90 tallafin da gwamnatin Tarayya ta ba hukumar domin aikin Hajjin bana baya ga naira miliya 8 da ɗori da kowani alhaji ya biya ba.
Jaridar Guardian ta buga cewa jami’an hukumar ICPÇ din sun dira hukumar inda suka zarce kai tsaye zuwa ofishin darektan harkokin kuɗi na hukumar domin gudanar da bincike.
Kakakin hukumar ICPC Dele Bakare ya shaida wa Guardian cewa aiki ne ya kai su hukumar, bayan sun rika gayyatar Darektocin hukumar amma suna kin amsa gayyatar.
” Bayan mun gayyaci wasu daga cikin darektocin hukumar ne suka ki zuwa, shine mu da kan mu muka zo muka waske da su zuwa hukumar domin su yi mana fillafilla game da wasu abubuwa da suka shige mana duhu.
Majiya ta ce sai da suka yi awoyi masu yawa a hukumar suna binciken takardu, bayan sun jide su sannan suka tasa keyar wani darekta suka tafi da shi domin amsa tambayoyi
Tun kafin a kammala aikin Hajjin 2024, shugaban hukumar Jalal Arabi ya fara fuskantar ƙalubale daga wasu manyan ƴan Najeriya da ma wasu Alhazai kan yadda ya gudanar da aikin Hajji a bana.
An samu korafe-korafen da dama daga Alhazai da ma’aikata da suka yi aiki a bana karkashin jagorancin Arabi.
Discussion about this post