Wasu ƙwararrun masana sun yi kira da a bijiro da sahihiyar turbar da za a shata wa ƙananan hukumomi, domin a tabbatar da bin ƙa’ida tare da yin taka-tsantsan wajen kashe kuɗaɗen su.
Hakan na zuwa ne bayan da Kotun Ƙoli ta bai wa ƙananan hukumomi 774 ma ƙasar nan, ‘yancin cin gashin kan su.
Masanan sun bayar da waɗanda shawarwari ne a ranar Litinin, a wani taron da ciniyar masana ta Agora Policy da ke Abuja ya shirya, tare da haɗin guiwar Hukumar EFCC, PREMIUM TIMES, BudgIT Foundation, Yiaga Africa, CFTPI da kuma The Cable.
A taron mai take: “Ɗanbaƙa Bin Ƙa’ida Wajen Tafiyar da Mulkin Ƙananan Hukumomi a Najeriya,” an gudanar da shi ne a Cibiyar Taruka ya Shehu ‘Yar’Adua da ke Abuja.
Cikin waɗanda suka bayar da gudummawar bayanai sun haɗa da Farfesa Remi Aiyede na Jami’ar Ibadan, Samson Itodo Babban Daraktan Yiaga Africa, Bukky Shonibare, Babbar Daraktar Invictus Africa, sai kuma Daraktan Riƙo na Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomin Najeriya, ALGON, wato Salawu Ozigi, wanda ya wakilci Shugaban ALGON, Aminu Maifata.
Nabillah Usman ta Radio Now ce ta gabatar da masu jawaban da kuma kiran tattaunawar.
An gudanar da taron sakamakon hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, inda ta ce a riƙa tura wa ƙananan hukumomi kuɗaɗen su kai-tsaye, a daina bayar da kuɗaɗen su a hannun gwamnan jiha.
Itodo ya ce bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai ba shi kaɗai ba ne mafita ba. Ya ce akwai buƙatar sanin wanda zai riƙa ɗora waɗannan ƙananan hukumomi kan turbar kasafin kuɗi da kuma yadda za su riƙa tafiyar da ayyukan.
Ita kuwa Shonibare kokawa ta yi dangane da ƙarancin mata kan muƙaman da aka fito aka samu ta hanyar zaɓe.
Ta ce, a 2015 akwai shugabannin ƙananan hukumomi 355 a jihohi 19, a wata ƙididdiga da Invectus Africa ta yi.
Ta ce amma a cikin su 16 ne kaɗai mata Shugabannin Ƙananan Hukumomi a lokacin.
EFCC Za Ta Zuba Masu Idanu Da Bibiyar Su – Olukoyede:
Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede, wanda ya samu wakilci daga Daraktan Tsara Ayyukan Musamman na EFCC, Friday Ebelo, ya ce hukumar sa na sa-ido sosai kan ƙananan hukumomi.
Tun da farko Babban Daraktan Agora Policy, Waziri Adio, ya ce jama’a sun dawo daga rakiyar yin amanna da ƙananan hukumomi a shekarun baya.
Ya ce a yanzu kashi 28 bisa 100 na mutane ke ganin ƙimar tsarin ƙananan hukumomi, saɓanin a baya cikin 2000 kashi 58 bisa 100 ke da yaƙini kan ƙananan hukumomi.
Discussion about this post