Gwamnatin Jihar Filato ta saka dokar hana fita kwata-kwata tsawon sa’o’i 24 a kullum, a cikin garin Jos da Bukuru, biyo bayan ganin yadda zanga-zanga ta rikiɗe zuwa ‘kwasar ganima’ a ranar Lahadi.
Cikin wata sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnan Filato, mai suna Gyang Bere ya sa wa hannu kuma ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi, Gwamna Caleb Mutfwang ya ce an ƙaƙaba dokar ce domin kare rayukan jama’a da dukiyoyin su, kuma a daƙile masu karya doka da oda.
“Gwamnan Jihar Filato, Celeb Mutfwang ya saka dokar hana fita baki ɗaya sa’o’i 24 a kullum, a cikin garin Jos da Bukuru, tun daga 12 na dare a ranar Lahadi, 4 ga Agusta, 2024.
“Gwamnan ya ɗauki wannan matakin gaggawa ne ganin yadda wasu ɓatagari suka far wa kayan jama’a da sata.
“Gwamnan ya lura da yadda ɓatagarin masu ɗauke da diga, adduna da sauran muggan makamai suka riƙa fasa kantinan jama’a da gidajen cin abinci a kan titin Bauchi Road, Zololo Junction a cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, suka riƙa sata da jidar kayan jama’a, kamar abinci da sauran kayayyaki.”
Gwamnan ya umarci jami’an tsaro su tabbatar da ana bin doka da oda a Jos da Bukuru da ma jihar baki ɗaya.
Discussion about this post