Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Afrika CDC ta ayyana cutar ƙyanda ‘Monkey pox’ a matsayin gagarimar matsala da ke neman ya mamaye nahiyar idan ba a yi gaggawar ɗaukar mataki a kai ba.
Shugaban cibiyar Jean Kaseya ya sanar da haka ranar Talata a taron da cibiyar ta yi da manema labarai domin neman madafa kan yadda za a dakile yaduwar cutar.
Zuwa yanzu cutar ta barke tare da yin ajalin mutane da dama a Nahiyar Afrika.
Mai nazari kan yaduwar cututtuka Salim Karim ya ce “Rashin iya yin gwajin cutar yadda ya kamata, rashin gudanar da bincike domin gano yadda cutar ke yaduwar, yawan mutanen dake kamuwa da dai sauran su na daga cikin matsalolin da ake fama da su a Nahiyar.
Karim ya ƙara da cewa cutar ta ci gaba da yaduwa a Afrika sannan yawan mutanen da cutar ke kashewa ya karu daga kashi 3% zuwa 4% sannan ana zaton hakan na da nasaba ne da yadda masu fama da cutar Kanjamau ke daɗa kamuwa da cutar.
Ya yi kira ga kasashen duniya, kungiyoyin Bada tallafi da su hada hannu da Afrika wajen yakar yaduwar cutar domin rashin yin haka ka iya zama babban matsala a duniya.
Yaduwar Cutar Monkey pox
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Afrika CDC ta ce an samu Karin kashi 160% a yaduwar cutar a shekarar 2024.
A ranar 28 ga Yuli rahotanni sun nuna cewa an samu mutum 14,250 da ake zaton sun kamu da cutar amma sakamakon gwaji ya nuna cewa mutum 2,745 daga cikinsu ne suka kamu da cutar sannan mutum 456 sun mutu a kasashen Afrika 10.
A Najeriya mutum 24 sun kamu sannan babu wanda aka rasu amma a kasar DRP mutum 13,791 sun kamu sannan mutum 450 sun mutu.
Bayan haka Nahiyar Afirka ta shirya tsaf domin ayyana dokar taɓaci yayin da barkewar cutar ke ci gaba da yaɗuwa a ƙasashen duniya.
Shugaban hukumar CDC Jean Kaseya ya ce ayyana dokar taɓacin zai taimaka wajen haɗa kan shugabannin kasashen Afrika wajen hada karfin da karfe domin yakar cutar.
Discussion about this post