Sai da Mariam Biliyaminu mai shekaru 12 ta daddage cikin ƙuncin rayuwa ta kai aji huɗu a firamare. Amma yayin da malejin tsadar rayuwa ya cilla sama daga ƙunci ya kai raɗaɗi, tilas Mariam ta kakare, daga Nuwamba 2023 har yau ba ta ƙara samun faragar zuwa makaranta ba.
Idan ana ta batun neman abin da za a bai wa ciki ya ya samu abinci, ba a ta batun karatu.
Mahaifiyar Mariam mai suna A’isha, ta ce ta cire yarinyar daga makaranta domin ta rage kashe kuɗaɗen da ba ma samuwa suke yi ba. Ta ce har gara ma Mariam ta haƙura ta zauna a gida ta riƙa taya ta aiki, tunda makarantar dama nisa gare ta. Kuma ga shi yaran marayu ne, a yanzu ba su da uba.
“Na cire ta na ce har gara sauran ƙannen ta su ci gaba da karatun, ita kuma Mariam ta riƙa taimakon ta kula da gida da kuma kula da sauran yaran idan na fita fafutikar nema.
“Miji na ya yi tafiyar sa ya bar ni da gaganiya da yara nan a Madallah, kuma ni ne cin su da shan su. Gaskiya rayuwa fa ta yi tsanani sosai. Aikatau nake yi ina sharar gidaje ana biya na. Kuma ina soya awara da sassafe, yara da ma’aikata masu fita aiki da wuri su na saye.”
Ta ce ta cire Mariam daga makaranta ne saboda a kullum sai ta biya mata Naira 400 kuɗin mota, sai kuma Naira 100 da za ta ɗan ci wani abu a makaranta.
Ita kuwa Bilkisu Iliyas, wadda maƙauta ke kira Umman Fridausi, ita ma cire jikar ya mai suna Hawwa daga makaranta ta yi, tun ta na firamare aji ɗaya, lokacin ta na shekara bakwai, a Ƙaramar Hukumar Bosso, Jihar Neja. Yarinyar ta na tsakiyar zuwa makaranta sai Boko Haram suka zama barazana ga yankin.
Cikin Yuli 2023, sai Bilkisu ta ɗauki Hauwa, ta kai ta hannun wani ƙanin ta mai suna Sheriff a Suleja. Kuma shi ma ba wani ƙarfi gare shi ba, birkila ne.
Mahaifin Hauwa shi ne babban ɗan Bilkisu. Ya rasu a wani hatsari. Ita kuma mahaifiyar ta, ta na can Bosso da zama.
Kafin a cire Hauwa daga makaranta, sai da hatta yinifom na makaranta sai da suka gagare ta.
Matsalar Yara Masu Gararambar Rashin Zuwa Makaranta A Jihar Neja:
Ƙididdiga ta nuna cewa kashi 40 bisa 100 na yaran Jihar Neja ba su karatu. Wato dai a duk cikin yara 5, to 2 ba su zuwa makaranta. Haka dai ƙididdigar UNICEF ta nuna a rahoton 2023.
Jihohi 8 ne da Abuja suka fi Jihar Neja taɓarɓarewar ilmin ƙananan yara a Najeriya.
Rahoton. UNICEF ya ce kashi 42 na yara mata ne ba su zuwa makaranta a Neja, maza kuma kashi 39 bisa 100.
Binciken da wannan jarida ta yi ya nuna jarida ta gudanar ya nuna cewa raɗaɗin tsadar rayuwa da rashin ɗaukar ilmi da muhimmanci a ɓangaren gwamnati da kuma rashin wadataccen albashin malamai da lalacewar ajujuwan karatu ne suka haddasa wannan matsala a Jihar Neja.
Discussion about this post