Sanatan Barno ta Kudu, Ali Ndume, ya nemi afuwar jam’iyyar APC, dangane da caccakar da ya yi wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
CIkin watan Yuli ne Ndume ya ragargaji Tinubu, inda ya ce wasu ‘yan ba-ni-na-iya sun kewaye shi, sun yi masa katanga daga sanin halin da ‘yan Najeriya ke ciki.
Ndume ya nemi afuwar kalaman da ya yi amfani da su ne, bayan ya gana da Shugabannin APC, ranar Talata, a Abuja.
Bayan ya caccaki Tinubu ne sai Shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Sakataren APC, Basiru Ajibola suka aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, suka nemi a cire Ndume daga a matsayin sa na Bulaliyar Majalisar Dattawa.
Jam’iyya ta nemi a maye gurbin sa da SanataTahir Monguno, na Barno ta Arewa.
Yayin da aka karanta wasiƙar da APC ta aika a majalisa, akasari duk suka amince da cire Ndume, kuma aka cire shi ɗin.
Saidai kuma bayan ya ziyarci Hedikwatar APC a ranar Talata, Sanata Ndume ya bayyana cewa ya yi kuskure da bai nemi izni daga shugabannin APC kafin ya ragargaji Tinubu ba.
Sai dai ya ce ya yi sukar ce a matsayin sa na mai cikakken kishin ƙasar nan. Kuma zai tabbatar nan gaba kafin ya ragargaji gwamnati ko shugaban ƙasa, sai ya nemi izni daga uwar jam’iyya tukunna.
Cikin watan Yuli Sanata Ndume ya sake nanata cewa, “na faɗa na ƙara faɗa, an yi wa Tinubu katangar rashin sanin halin da ‘yan Najeriya ke ciki”.
Kalaman Ndume Waɗanda Ya Janye:
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa shi fa bai yi wani laifi ba don kawai ya caccaki salon mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
A kan haka ya ce shi dai ba zai bada haƙuri ba, kuma ba zai nemi afuwa ga kowa ba, duk kuwa da cire shi daga muƙamin Bulaliyar Majalisar Dattawa da aka yi.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya cire Ndume daga Bulaliyar Majalisar Dattawa, bayan ya samu daga Shugaban APC, Abdulalhi Ganduje.
A cikin wasiƙar, Ganduje ya yi wa Akpabio matashiya da kwafen hirar da aka yi da Ndume, inda ya ragargaji Tinubu da gwamnatin sa.
A yanzu bayan cire shi daga muƙamin Bulaliyar Majalisar Dattawa, Ndume ya ce har yanzu ya na nan kan bakan sa, kuma ba zai nemi afuwar kowa ba.
A wani bidiyon da Gidan Talabijin na Channels ya watsa, Ndume ya ce shi fa ya fi ƙarfin gori a APC, domin tare da shi aka kafa jam’iyyar.
Ya kuma yi watsi da rahoton cewa an ba shi wani kwamiti a yanzu a Majalisar Dattawa.
“Dangane da abin da ya faru na sake sauraren tattaunawar da aka yi da ni. Kuma na watsa intabiyu ɗin da kai na ga abokai, yayye da shugabanni. Na ce su saurara kowa ya faɗa min inda ban yi daidai ba. Su faɗa min inda na yi ƙarya.
“Kuma mutanen da na tura wa kowa ya ce min ya saurara, amma babu inda na yi kuskure. Saboda haka na je na faɗa ɗin, na kuma ƙara faɗa. Ina nan kan baka na dangane da dukkan abin da na furta cikin tattaunawar,” cewar Ndume.
“Ina kuma ƙara faɗa a yanzu haka cewa ba kishin ƙasa ba ne mutum ya riƙa goyon bayan duk wani abin da shugaban ƙasa ya yi, ko da ya aikata ba daidai ba.
“Ya kamata mutum ya riƙa faɗin gaskiya ba ma ga shugaban ƙasa kawai ba, har ma ga kowa.
“Maganar gaskiya mutane na cikin wahala fa. Kuma mutane sun hasala. Na ji daɗi da Shugaban Ƙasa ya maida mafi ƙanƙantar albashi zuwa Naira 70,000. To amma kuma kamata ya yi a ce sun wuce haka. Domin 70,000 ɗin nan fa kuɗin buhun shinkafa ne. Saboda haka ina kira ga Shugaban Ƙasa ya riƙa sauraren jama’a.”
Discussion about this post