Tsohon Gwamnan Kano, kuma tsohon Ministan Ilmi, Ibrahim Shekarau, ya ce bai taɓa karɓar ko sisin kwabo daga hannun ɗan kwangila ba.
Shekarau wanda ya yi sanata daga 2019 zuwa 2023, ya bayyana haka a ranar Laraba, a wurin taron manema labarai, domin cikar Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN) cika shekaru 70 da kafuwa.
Shekarau ya ƙara da cewa kuma har ya yi gwamna ya kammala shekaru takwas bai taɓa cirar kuɗaɗen ƙananan hukumomi ba.
“Na fada maku a zamanin gwamnati na na sha magana kan batun cin kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
“Ba zan ce Ni kaɗai ba ne, amma dai idan ma akwai wasu, ina cikin ƙalilan na gwamnonin da ba su taɓa cin ko sisi na ƙananan hukumomi ba.
“Kuma a shekaru 44 da na yi ina aikin gwamnati, ban taɓa shirya yadda zan karɓi ko sisi daga hannun wani ɗan kwangila ba.
“Ina alfahari da cewa ban karɓar ko sisi daga hannun wani ɗan kwangila ba. Kuma duk su na nan da ran su. Ba ni da komai sai gidan da mallaka a Kano.
“Gidan da na ke zaune Abuja ma na haya ne. Duk ma samu wannan tarbiyya daga dalilin shiga ta MSSN tun tuni.”
Discussion about this post