Ofishin Jakadancin Rasha na Najeriya ya nesanta ƙasar sa daga hannu ko alaƙa ta kusa ko ta nesa da waɗanda suka riƙa filfila tutar ƙasar a lokacin zanga-zanga a faɗin Najeriya.
A zanga-zangar ta ranar Litinin, an riƙa filfila tutar Rasha a wasu garuruwan Arewa, yayin da ake ta kiraye kirayen a cire Shugaban Ƙasa Bola Tinubu daga kan mulkin Najeriya.
Gwamnatin Najeriya dai ta ce ba za ta lamunci kiraye-kirayen sojoji su ƙwace mulki ba, kuma duk wanda ya filfila tutar wata ƙasa to ya aikata laifin cin amanar ƙasa.
Haka dai Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Christopher Musa ya bayyana.
A cikin sanarwar da Ofishin Jakadancin Rasha da ke Najeriya ya fitar a ranar Litinin, ya ce, “Gwamnatin Rasha da dukkan jami’an gwamnatin ba su da hannu ko alaƙa da masu filfila tutar Rasha, kuma ba su tsara masu yin hakan ba.
“Kamar yadda a kullum mu ke jaddadawa, ita fa Rasha ba ta yin katsalandan ɗin shiga harkokin cikin gida na wata ƙasa ko a ina, kuma har da Najeriya.
“Filfila tutar Rasha da wasu masu zanga-zanga suka yi, wannan ra’ayin su ne, kuma bai yi daidai da ra’ayin ko ɗaya daga cikin tsarin mu ko manufofin Gwamnatin Rasha ba.”
Rasha ta ƙara da cewa, “muna girmama Najeriya tare da ganin ƙimar ƙasar da dimokraɗiyyar da take bisa turba.
“Saboda haka mun yi amanna cewa zanga-zangar lumana na bisa tsari na dimokraɗiyya, kamar yadda dokar Najeriya ta jaddada.
“To amma idan zanga-zanga ta rikiɗe zuwa tarzoma da tayar da hankula, to muna yin tir da ita.”
Discussion about this post