Da alama yaƙin cacar-bakin da ake fafatawa tsakanin Abdulmumin Jibrin-Kofa da Ado-Doguwa, ya sake ɗaukar sabon salo inda Kofa ya sake mayar masa da zazzafan martani. Kofa dai ya tsaya kai da fata sai Doguwa ya nemi afuwa kan yadda yake yawan zagi da yin ƙage ga Jagoran NNPP na ƙasa, kuma Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Kwankwaso, sannan ya daina zagin sa ya kuma girmama shi kamar yadda shi Kofa yake girmama shugabannin jam’iyyar sa APC.
A raddin baya-bayan nan dai Doguwa yi wa Kofa gorin cewa shi dai ya ci zaɓe ba tare da jingina da Kwankwaso ba.
Shi kuma Jibrin-Kofa, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta bakin Hadimin Yaɗa Labarai, Sani Ibrahim-Paki, ya ce a bayyane take cewa Doguwa bai taɓa lashe halastaccen zaɓe ba a tarihin siyasar sa, sai dai ta hanyar maguɗi da tayar da tarzoma, lamarin da yake jefa mutanen mazaɓar sa cikin halin takaici, hawaye har ma da zargin zubar da jini.
Kofa ya kuma ce a kullum Doguwa na wakiltar mutanen sa ne ta ƙarfin tsiya da kuma kama-karya, a samfurin mulkin da za a iya kwatantawa shi da na Idi Amin na ƙasar Uganda.
Ɗan majalisar ya ce kasancewar Doguwa a Majalisar Wakilai har sau bakwai a tsawon shekaru 32 da kuma yadda yake bugun ƙirjin dukkan muƙaman da ya riƙe a rayuwar sa a cikin majalisar suke, a daidai lokacin da yanzu haka akwai waɗanda ya kusa yin jikoki da su a majalisar, kamata ya yi a ce shi jam’iyyar sa ta sahale wa ya nemi shugabancin majalisar, kamar yadda ta yi wa wanda ya jagoranci majalisar da ta gabata.
Amma duk da cewar Doguwa ne mutum na farko da ya bayyana buƙatar sa ta neman kujerar tun kimanin shekaru biyu kafin ƙarewar wa’adin wanda ke kai a lokacin, a wani yanayin da ba a taɓa ganin irin sa ba a tarihin majalisar, “sai ga shi kowa ya san yadda jam’iyyar sa ta nesanta kanta daga takarar Doguwa, saboda yadda zargin kisan ’yan mazabar sa a lokacin zaɓe ya dabaibaye shi. Kuma a yanzu kowa na jiran ya ga abin da ɓangaren shari’a zai yi a kan lamarin.
“Kazalika, jam’iyyar sa ba ta ga dacewar sa ya zama Mai Tsawatarwa ko Shugaban Masu Rinjaye ba a 2023. Muƙamai biyu muhimmai da ya taɓa rikewa a baya, waɗanda kuma Allah ne shaida, ni na taka muhimmiyar rawa wajen kasancewar sa a kan su, inda na kyautata masa zaton zai canza hali. Amma ina, ya gaza ba maraɗa kunya,” inji Kofa.
Ya kara da cewa, “a zahirin gaskiya, duk da dai ya yaƙe mu a lokacin zaɓen Kakakin Majalisa a 2015 da 2019, waɗanda na kayar da shi a duka biyun, ni kaɗai, bisa umarnin Kwankwaso, na tallata shi har aka zaɓe shi Mai Tsawatarwa na Majalisa a 2015, sannan na sake yi masa haka a 2019, bayan na jagoranci zaɓen Kakakin Majalisa, inda muka ɗora shi Shugaban Masu Rinjaye bisa umarnin Gwamnan Kano na wancan lokacin, mutane biyun da daga bisani ya ci amanar su kuma yake ci gaba da yaƙar su, ko sun sani ko ba su sani ba.
“Doguwa ne cikakken cima-zaunen da ya je Majalisa ba shi da komai, ƙafafun sa sanye da silifas, amma yake ci gaba da zama matsala ga siyasar Kano da ma ta ƙasa baki ɗaya, inda yake kawo rarrabuwar kai tsakanin shugabanni da jama’a kuma yake tunzura jama’a don biyan bukatar sa. Muddin ana son samun zaman lafiya a Kano, sai an yi maganin Doguwa, an gane shi da halin sa, a matsayin sa na cikakken maci-amana, mai fuska biyu, mai bambaɗanci, mara tausayi kuma maƙaryaci, wanda cikin kusan dukkan maganganun sa 10, guda tara daga ciki ƙarairayi ne tsagwaron su.
“Don haka ba abin mamaki ba ne idan ya bi kowacce irin hanya, ciki har da zargin zubar da jinin mutane, domin buƙatar sa ta siyasa ta biya.”
Ya kuma ce Doguwa mutum ne da ya tasam ma nitsewa a kogin tarihi, wanda yake neman suna ko ta wane hali bayan rashin ƙwarewar sa akan shugabancin Kwamitin Harkar Mai ta bayyana a idon duniya, sannan an toshe duk wata hanya da yake bi ta ganin ido.
Discussion about this post