Wata majiyar tsaro a Najeriya ta sanar wa JaridarTHE WHISTLER cewa Ƴan kungiyar shi’a ne suka kutsa cikin masu zanga-zanga a wasu garuruwan arewacin Najeriya suka yamutsa tafiyar masu zanga-zangar na ainihi.
An gano cewa ƴan shi’an dake Ƙarƙashin kungiyar IMN ne su kutsa cikin masu zanga-zanga na ainihi suka saje dasu, kuma sune suka rika ɗaga tutocin Rasha yayi tattaki da masu zanga-zanga ke yi a musamman biranen Kano, Jos da Abuja.
A Kano, daruruwan matasa masu karancin shekaru sun fito kan titunan Kano a ranar Alhamis din da ta gabata, suna kira ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da ya sa baki a Najeriya. Wasu daga cikinsu sun yi kira da a yi juyin mulkin soja.
A ranar Asabar din da ta gabata ma sun bijirewa dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnatin jihar ta kafa inda suka bi jerin gwanon masu zanga-zanga cikin birnin ɗauke da kwalaye da rubuce-rubucen kira ga sojojin Rasha su kwace mulkin Najeriya.
An lura da irin haka a Abuja, babban birnin kasar da kuma Jos, babban birnin jihar Filato yayin zanga-zangar da ake yi.
Majiya daga gidan gwamnatin Jos ta shaidawa THE WHISTLER cewa gwamnatin jihar na sane da cewa wasu kungiyoyi da aka ɗauki nauyin su sun kutsa cikin masu zanga-zangar domin yamutsa abin.
“Kafin Gwamna Caleb Mutfwang ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a birnin Jos-Bukuru a ranar Lahadi, ya gargadi shugabannin al’umma cewa wasu kungiyoyin da aka dauki nauyin su sun kutsa cikin Zanga-Zangar kuma za su mamaye Zanga-Zangar. inji majiyar.
Jaridar WHISTLER ta kara da cewa fitaccen Dattijo, a Kano, Alhaji Tanko Yakasai a hira da yayi da jaridar ya ce waɗanda ba su ƙaunar Najeriya ne suke ruruta wutar tashin hankali a ƙasar ta hanyar amfani da Zanga-zanga.
” Akwai wadanda ba su ƙaunar Kasar nan, kuma sun sha alwashin sai sun yamutsa. Sune ke fakewa da wannan zanga-zanga suna neman hargitsa kasar, zaman lafiya ya gagari kowa.
A jihohin Kaduna ma, kafin gwamnati ta saka dokar hana walwala, masu zanga-zangar sun rika ɗaga tutar Ƙasar Rasha yayin da suka tattaki a cikin birnin Kaduna.
Discussion about this post