Domin tabbatar da daidaiton farashin man fetur da kuma farashin Dala da Naira, a yau Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da kudirin da Shugaba Tinubu ya gabatar na sayar da danyen mai ga Matatar Dangote da sauran matatun mai da ke tafe a Naira.
Matatar Dangote a halin yanzu tana bukatar tulin kago 15 na danyen mai, akan kudi dala biliyan 13.5 duk shekara. Kamfanin NNPC ya kuduri aniyar samar da guda hudu.
Sai dai majalisar zartaswar ta amince da cewa ganga 450,000 da za a yi amfani da su a cikin gida za a ba da su a cikin Naira ga matatun man Najeriya, ta hanyar amfani da matatar Dangote a matsayin na farko. Za a daidaita ƙimar musanya na tsawon lokacin wannan ciniki da zarar an fara bada man.
Wannan matsayi da gwamnati ta ɗauka zai kawar da matsalar musayar canji da kasa ke fama da shi sannan kuma naira za ta yi daraja kuma farashin mai a gidajen mai zai karye maruƙa.
Discussion about this post