Babbar tawagar kwallon kafa ta Sipaniya ta kai wasan karshe na kofin Nahiyar Turai EURO 2024, bayan doke Faransa da ci 2-1 a birnin Munich.
Lamine Yamal da Dani Olmo ne suka ci wa Sifaniya kwallayen da ta ba su wannan nasarar.
Kafin hakan dai ɗan wasan gaban Faransa Kolo Muani ne ya fara ci wa Faransa kwallo a mintina na 8 da take wasa, daga bisani Sifaniya ta rama ta hannun Lamine Yamal, sannan ta ƙara ta biyu dul kafin hutun rabin lokaci da hannu Olmo a mintina na 25.
Da wannan nasarar yanzu haka Sifaniya ta yi nasara sau 17 a kan Faransa a wasannin da suka buga a tsakanin su, yayin da Faransa ta yi nasara kan Sifaniya sau 13, kuma suka yi canjaras a wasanni bakwai.
Yanzu haka dai, Sifaniya tana jiran kungiyar da zasu buga wasan ƙarshe tsakanin Netherlands da England wanda zasu kara a ranar Laraba da ƙarfe 8 na dare, a flin wasa na Signal Aduna Park dake Dortmund.
Za a buga wasan ƙarshe na Kofin EURO 2024 a filin wasa na Olympiastadion dake Berlin, Jamus, a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuli 2024 da karfe 8 na dare.
Daga: Muhammad Suleiman Yobe
Discussion about this post