Iyalan tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, sun ɗaukaka ƙarar hukuncin da kotu jaddada ƙwace masu filin da Abacha ɗin ya mallaka tun shekaru takwas kafin rasuwar sa.
Abacha ya mallaki filin tun a ranar 25 ga Yuni 1993, lokacin ya na Ministan Tsaro. Ya zama Shugaban Ƙasa cikin watan Nuwamba, 1993 watanni biyar bayan ya mallaki filin.
Cikin watan Fabrairu 2006 ne Hukumar FCDA Abuja ta soke satifiket ɗin filin, a zamanin tsohon Ministan Abuja, Nasir El-Rufai. Wato shekaru takwas bayan rasuwar Abacha a cikin Nuwamba, 1998.
Tun bayan soke filin ne iyalan Abacha ke ta haƙilo a kotu, su na neman a sake mallaka masu haƙƙin su.
A ranar Litinin ce Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ce iyalan Abacha sun makara kuma sun makaro daga neman haƙƙin mallakar filin wanda ke cikin unguwar Maitama. Saboda tun a cikin 2015 kotu ta yi watsi da neman haƙƙin na su.
Ganin cewa ba su gamsu da wannan hukunci ba, sai Maryam Abacha da Mohammed Abacha suka sake ɗaukaka ƙara a ranar Talata.
Sun shigar da FCDA kotu tare da Shugaba Tinubu, Salamed Ventures waɗanda yanzu su ne aka mallaka wa filin.
Lauyan su Reuben Atabo (SAN) ya shigar da dalilai da hujjojin ɗaukaka ƙara har guda 11.
Tun a cikin watan Mayu ne dai kotu ta sa ranar yanke hukunci, wanda bayan an yanke ɗin bai yi wa iyalan Abacha daɗi ba.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayyana cewa za ta yanke hukunci a ranar 27 ga Yuni, a ƙarar da iyalan marigayi tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Abacha suka shigar.
Iyalan Abacha sun shigar da ƙarar rashin amincewa da soke satifiket na wani gini da gwamnati ta ƙwace, wanda mallakar su ne a Maitama, cikin Abuja.
Mai Shari’a Peter Lifu ya sa ranar ce domin yanke hukunci, bayan lauyan iyalan Abacha, Reuben Atabo (SAN) da lauyoyin gwamnati bisa jagorancin James Onoja (SAN) suka kammala bayanan su.
Idan za a iya tunawa, tun cikin 2006 aka ƙwace ginin, shekaru kisan takwas bayan mutuwar Abacha.
Maryam Abacha, uwargidan marigayin ce da ɗan ta Mohammed Abacha suka shigar da ƙara.
Sun maka Ministan Babban Birnin Tarayya kotu, shi da Hukumar FDCA, Gwamnatin Tarayya da kamfanin Salamed Ventures Limited.
Maryam da ɗan ta Mohammed na so kotu ta janye ƙwace masu gini da aka yi, ta maida masu abin su.
Lambar satifiket ɗin filin dai ita ce FCT/ABUKN 2478, mai lambar fili na 3119. An damƙa shi tun cikin 1993, a ranar 25 ga Yuni.
Iyalan Abacha sun ce an ƙwace masu filin ba bisa ƙa’ida ba, ta haramtacciyar hanya aka ƙwace masu shi, cikin 2006 zamanin da Nasir El-Rufai ke Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Discussion about this post