Kungiyar shugabannin hukumomin Alhazai ta jihohi sun nuna rashin amincewar su da kira da gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi na a rage wa hukumar Alhazai ta kasa ƙarfi ta yadda wasu abubuwan jihohi za su iya ɗaukar nauyinsa kai tsaye.
Idan ba a manta ba, gwamna Bala ya nuna bacin ransa a lokacin da yake rangadin rumfunan Alhazan Bauchi a Muna, inda ya ce Hukumar Alhazai ta kasa ta gaza a wurare da dama da jakan ya jefa alhazai cikin tsananin wuya a wasu lokutta da dama yayin aikin Hajji.
Ya ce abinda ya fi dacewa shine a rage wa hukumar NAHCON karfi ta hanyar kyale jihohi suna ɗawainiyar wasu aiyukan mahajjatansu ba sai dole Hukumar Haji ta ƙasa ba.
Daga nan sai ya raba wa Alhazan jihar kyautar Riyal 300 kowannen su wanda ya yi daidai da naira 120,000 goron sallah.
Kafin nan ya bayyana cewa zai zauna da gwamnonin Najeriya domin su duba yiwuwar ganin yadda za a rage wa hukumar Alhazai karfi, jihohi su rika kula da Alhazan su a wasu ɓangarorin.
Faruq Aliyu, wanda ya yi jawabi a madadin kungiyar hukumomin Alhazan na jihohi ya bayyana cewa, ba su tare da gwamna Bala kan wannan batu.
Aliyu ya ce cikin kashi 100 NAHCON ta yi abin yaba na sama da kashi 80 a aikin Hajjin bana.
” Saboda haka mun yaba wa hukumar sannan muna jinjina mata bisa nasarorin da ta samu tun daga farkon fara aikin Haji na bana zuwa yanzu.
” Sannan kuma maganan wai a rage wa hukumar Alhazai karfi bai ma taso ba domin, yadda tsarin ya ke ba ma zai yiwu a jihohi su iya ba.
Discussion about this post