Hukumar FCT Abuja ta bayar da wa’adin sa’o’i 24 kacal domin fara rushe duk wasu haramtattun gine-ginen kasuwannin da ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ƙananan matsugunai akan hanyar Karmo zuwa Deidei.
Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa an shafa wa gine-gine da matsugunai sama da 500 jan fentin da ke nuna cewa za a ruguje wurin.
Babban Jami’in Rusau, Garba Jibril da Mataimakin Darakta mai jagorar aikin rusau a Abuja, sun bayyana cewa an sha yi wa masu wuraren da za a rusa ɗin gargaɗin tashi, ba sau ɗaya ko sau biyu ba.
Jibril ya ce Daraktan Kula da Gine-gine, Muktar Galadima ya yi taron ganawa da waɗanda lamarin ya shafa.
Ya ce rushe wurin ya zama wajibi, saboda ana haifar da cinkoso kan titi ma manyan motocin ɗaukar kaya, musamman a ranakun kasuwa.
Kuma ya ƙara da cewa harkokin da ake yi a wurin su na haifar da gurɓata muhalli, wanda Hukumar FCT Abuja ba ta amince da hakan ba.
Ya ce an bayar da aikin shimfiɗa kwalta daga Camp zuwa Dei-dei, amma harkokin da ‘yan tireda ke yi kan hanyar sun hana masu aikin hanyar zuwa su fara.
Ya ce duk wanda bai kwashe kayan sa cikin sa’o’i 24 ba, to ya kuka da kan sa.
Ya ce tuni aka umarci masu kasa kaya kowa ya je ya kama shago a kasuwar Karmo, domin ta na da kayan inganta rayuwa wanda ake buƙata.
“Amma ‘yan tiredar sun ƙi komawa, mun yi ganawa da su ba sau ɗaya ko sau biyu ba. Har mun yi amfani da shugabannin masarautu na yankin, muka sa su shawarce su su tashi, amma suka yi banza da su.
“Mun gana da ‘yan tiredar da masu gudanar da kasuwar, waɗanda suka yi alƙawarin bai wa masu tiredar wuraren zama a cikin kasuwar.”
Discussion about this post