Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta fara ƙoƙarin dakatar da Kakakin Majalisar Jihar Neja, Abdulmaliki Saekindaji shirin da yake yi na bada auren ‘yan mata 100 marayu a Jihar Neja.
Ta ce ta garzaya ta kai ƙorafi ga Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, kuma ta nemi kotu ta hana aure, har sai an kammala bincike tukunna.
Sarkindaji ya bayyana shirin da yake yi na bada auren ‘yan matan marayu, waɗanda suka rasa iyayensu sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Mariga, cikin Jihar Neja.
Kakakin Majalisar na Neja ya yi shirin bada auren su a ranar 24 ga Mayu, ya ce auren yaran da zai bayar na daga cikin ayyukan sa na mazaɓa.
“Zan yi haka ne domin rage masu ƙuncin rayuwa da talaucin da suke fama da shi,” cewar sa.
Ya yi alƙawarin zai biya sadakin kowace budurwa cikin ‘yan matan su 100, kuma shi zai sai wa kowace kayan ɗaki.
To amma Ministar Mata Uju ya ta shaida wa manema labarai a Abuja cewa wannan shiri “ba abin amincewa ba ne.”
Ya ce ya kamata a gudanar da bincike tukunna, kafin a zo kan maganar auren su da za a bayar.
“Ina so Mai Girma Kakakin Majalisar Jihar Neja ya sani cewa ba zai yiwu haka kawai Ma’aikatar Harkokin Mata da gwamnati su amince da wannan shirin ba!
“Saboda akwai Dokar ‘Yancin Ƙananan Yara, kuma tun farkon hawa na minista na ce an daina yin abu barkatai.
“Tilas a koma ta kan waɗannan ƙananan ‘yan mata. Tilas a dubi makomar su nan gaba tukunna.
“Saboda haka na garzaya kotu. Na rubuta takardar ƙorafi ga Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya.
“Na shigar da ƙara ina neman kotu ta dakatar da auren yaran har sai an gudanar da bincike. Shin da yardar su da amincewar su za a yi masu auren? Shekarun kowace a cikin su nawa kafin a yi mata aure? Su wane ne za su aure su?” Inji ta.
“Tunda shi Kakakin Majalisar Jihar Neja bai yi tunanin ilmantar da yaran ba, ko koyar da su sana’o’i ko wani jari, mu za mu ɗauki nauyin ba su ilmi. Wadda ke buƙatar koyon sana’ar dogaro da kai kuma mu koya mata, sannan mu ba ta kayan sana’a da jari. Sannan sai su yi tunanin lokacin da ya dace su yi aure.”
“Idan kuma Kakakin Majalisar Neja ya yi wani abu saɓanin haka, to za mu kwashi ‘yan kallon kwatagwangwamar shari’a, tsakanin sa da Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya.” Inji Minista Uju.
Discussion about this post