Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin hana gayyatar da Babbar Kotun Jihar Kogi ta yi wa Shugaban EFCC, a ƙarar da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya maka EFCC, tun a farkon wannan shekara.
Manyan Alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara bisa jagorancin Joseph Oyewole ne suka yanke hukuncin bada umarnin soke kiranyen da Kotun Kogi ta yi wa Shugaban EFCC, Olukoyede.
Lauyan Shugaban EFCC mai suna Jibrin Okutepa ne ya shigar da ƙarar, a madadin shugaban na EFCC.
Sauran masu yanke hukuncin sun haɗa da Mai Shari’a Peter Obiora da Mai Shari’a Okon Abang.
Lauyan Shugaban EFCC, Jibril Okutepa ne ya aika wa manema labarai da wannan hukunci da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke. Okutepa dai babban lauya ne SAN, kuma shi ne ya shigar da ƙarar, wadda aka yanke hukunci a ranar Juma’a.
Yayin da suke yanke hukunci, kotun ta soke kiranyen bayyana gaban kotu da Kotun Jihar Kogi ta yi wa Shugaban EFCC, domin ya amsa tuhumar zargin raina kotu, bayan ya ƙi halartar gayyatar da ta yi masa a baya.
Haka kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bada umarnin a je ƙofar gidan Yahaya Bello da ke kan Titin Bengazi Street, Wuse Zone 4, Lamba 9, a manna kwafen takardun hukuncin, cewa ta hana Shugaban EFCC bayyana a gaban Babbar Kotun Jihar Kogi.
Wannan hukunci ya nuna cewa yanzu abin da ya rage wa EFCC shi ne ta ci gaba da farautar Yahaya Bello, wanda take zargi da wawurar Naira biliyan 80 na jihar Kogi a lokacin da yake gwamna.
Har yanzu dai ta na cigiyar Bello tun bayan sanarwar arcewar da ya yi makonni biyu da suka gabata.
Discussion about this post