Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, Reshen Ofishin DPO na Rijiyar Lemo, ya kafa tsauraran sharuɗɗa 13 da tilas a cika su kafin a bai wa mutum iznin shirya taron kiɗan ‘DJ’ da sauran kaɗe-kaɗen al’adu, majalisi da sauran su.
Cikin wata sanarwar da suka fitar, a makon jiya, wadda Sheikh Lawan Triumph ya kasanta wa masu sauraron karatun sa a cikin masallaci, rundunar ‘yan sandan ta sanya wa sanarwar suna: “Idan Kunne Ya Ji, Jiki Ya Tsira!”
Sanarwar na ɗauke da cewa an yi haka ne domin tabbatar da kare lafiya, rayuka da dukiyoyin jama’a.
Sanarwa ta farko dai ta ce tilas wanda ya shirya buki ko taron ya je Ofishin ‘Yan Sanda da kan sa ya nemi izni, aƙalla kwana bakwai kafin ranar yin taron.
2. Wanda zai ɗauki nauyin shirya taron ne zai je da kansa neman izni, ba aike zai yi ba.
3. A tabbatar ba a shirya taron kan hanya, inda za a takura wa jama’a masu wucewa kan ababen hawa da masu wucewa a ƙasa ba.
4. A tabbatar an shirya taron a killataccen wuri.
5. Kada a kuskura a cakuɗu maza da mata.
6. A tashi daga taron minti 10 kafin kiran Sallar Magriba.
7. Kada a ci gaba da taron bayan Sallar Magriba.
8. Kada a yi shaye-shaye a wurin taron.
9. Wanda ya shirya taron shi zai tabbatar da tsaro a wurin taron, kafin a fara, lokacin da ake gudanar da taron da bayan tashi daga taron.
10. Tilas wanda ya shirya taron ya kai wanda ya tayar da rigima a wurin taron.
11. Ba a yarda wani ya shiga da makami ba.
12. Wanda ya shirya taron ya kai kan sa Ofishin ‘Yan Sanda idan aka yi faɗa kafin fara taron, lokacin da ake taron ko bayan tashi daga taron.
13. Hana rerawa ko kunna waƙa ko wani baiti mai ɗauke da zagi, cin zarafi, habaici, zambo, kai tsaye ko a fakaice kan wani.
Discussion about this post