Gwamnatin tarayya ta bada umarnin hana manyan asibitocin kasar nan amfani da allura da sirinji da aka shigo da su daga kasashen waje.
Gwamnati ta ce daga yanzu wadannan asibitoci za su rika amfani da allura da sirinjin da aka hada su a kasar nan kuma hukumar NAFDAC ta amince da su.
Wannan sako na kunshe ne a takardar dake dauke da sa hannun karamin ministan lafiya Tunji Alausa wanda ya fitar ranar Juma’a.
Ministan ya ce gwamnati ta bada wannan umarnin domin farfado da masana’antun yin allura da sirinji da ake da su a kasarnan.
Alausa ya ce matsalar shigowa da allura da sirinji daga kasashen waje na daga cikin matsalolin dake ci wa masana’antar hada magunguna ta kasar nan tuwo a kwarya.
Ya ce daga cikin masana’antun hada magunguna dake Samar da allura da sirinji 9 da ake da su a kasar uku ne kacal ke aiki.
Alausa ya ce gwamnati ta umarci hukumar NAFDAC ta dakatar da bayar da lasisin shigo da allura da sirinji daga kasashen waje zuwa Najeriya.
Ya ce gwamnati za ta soke jerin sunayen kamfanonin da ke da hannu wajen shigo da wadannan kayayyaki domin hana su ci gaba da aiki a kasar nan.
Discussion about this post