Shugaban rukunin jami’o’in Maryam Abacha, Farfesa Adamu Gwarzo, ya jagoranci tawagar masu ta’aziyyar rasuwar babban hadimin uwargidan tsohon shugaban kasan Najeriya, Maryam Abacha, marigayi Musa Yau a Katsina.
Musa ya rasu ranar Laraba a asibiti a Abuja, bayan fama da yayi da rashin lafiya.
Ya rasu ya bar ƴa’ƴa takwas, mahaifiyarsa da matarsa.
Farfesa Gwarzo wanda ya halarci sallar jana’izar ya garzaya zuwa ga iyalan mamacin bayan haka, inda ya yi musu ta’aziyya da kuma addu’o’in Allah ya ji ƙansa ya sa Aljanna ta zamo makomarsa.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin ta’aziyyar farko da farfesa ya aika wa iyalai da ƴan uwan mamacin a madadin sa da iyalan sa.
A wata sanarwa ta musamman daga Farfesa Gwarzo ranar Laraba, ya yi jimamin rasuwa marigayi Yau inda ya yi masa Addu’ar Allah ya sa Aljanna ta zamo makomansa.
” Mun yi rashi. A madadin jami’ar MAAUN, ina mika ta’aziyya ta ga uwargidan tsohon shugaban kasa, Maryam Abacha, bisa wannnan rashi da aka yi.
” Ina rikon Allah ya jiƙan Yau ya kuma sanya Aljanna ta zamo makomarsa Amin.
Discussion about this post