‘Yan matan Mariga 100 waɗanda aka dakatar da shirin yi masu auren-gata a Jihar Neja, sun bayyana rashin jin daɗin janyewar da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja Honorabul Sarkindaji ya yi.
Kakakin dai ya shirya gagarimin bikin yi wa ‘yan matan auren-gata, ta hanyar biya wa kowace sadaki, yi masu kayan ɗaki da kuma ba su jarin kama sana’a a gidan mijin su.
Sai dai kuma shirin wanda aka aza ranar gudanarwa a ranar 24 ga Mayu, ya samu cikas, sakamakon rashin amincewar da Ministar Harkokin Mata ta nuna, ta hanyar shigar da ƙara da kuma rubuta wasiƙar koke ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.
Hakan ta sa Sarkindaji ya fasa ɗaukar nauyin shirya wa ‘yan matan auren-gatan da ya yi niyyar yi masu.
‘Yan matan su 100 dai an tantance su ne daga ‘yan mata 170, inda aka zaɓi 100 daga cikin su.
An shirya yi masu auren-gata saboda sun rasa iyayen su sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a yankin Mariga na cikin Jihar Neja.
An shirya gudanar da bikin a garin Bangi, cikin Ƙaramar Hukumar Mariga.
An kuma tsara cewa Shugaban Hukumar Hisbah na Jihar Kano, Aminu Daurawa, shi ne zai jagoranci ɗaurin auren, wanda Gwamna Mohammed Bago da Sarkin Minna, Mohammed Barau za su halarta.
Yayin da ya janye ɗaukar nauyin shirin, Sarkin Daji ya ce dukkan ‘yan matan sun isa aure, kuma auren-gata ne zai yi masu, ba auren-dole ba.
Ya yi kira ga Ministar Harkokin Mata ta je ta kai ziyara yankin domin ta gane wa idon ta irin halin da su ke ciki.
‘Auren-gata Aka Shirya Yi Mana, Ba Auren-dole ba – Hussaina Abdullahi:
Hussaina ta na ɗaya daga cikin waɗanda aka yi niyyar gangamin ɗaurin auren su, amma aka janye.
Ta bayyana cewa ta cika da farin ciki ganin za a yi mata auren-gata. Ta ce ta yi niyyar auren saurayin ta saboda ƙaunar juna da soyayyar da ke tsakanin su da juna.
“Ba wanda ya tilasta cewa zai yi mana auren-dole. Mun jira zuwan wannan lokaci ne saboda rashin gata da rashin sukunin kuɗaɗe.”
Habibah Mohammed cewa ta yi ita ta zaɓi miji da kan ta, ba wanda ya tilasta mata. Ni na kawo shi da kai na, ba tilasta min shi aka yi ba.”
Mahaifiyar wata daga cikin ‘yan matan, mai suna Amina Umar, ta ce ita da mijin ta wanda ya rasu, sun yi ta fatan ganin ‘yar su ta yi aure.
“Tun shekarun baya muka so yi wa ‘yar mu aure, amma abin bai yiwu ba, saboda matsalar kuɗi.
Amina ta goyi bayan ƙoƙarin da Sarkindaji ya yi da wanda ya yi niyyar yi kafin a samu tsaiko.
Hakimin Mariga Shehu Mariga ya ce hare-haren ‘yan bindiga ya haddada yawaitar yara marayu a yankin su, har da ƙananan yara da dama.
“To wasu daga cikin yaran da aka mutu aka bari, sun girma, har sun isa aure amma ba su da mai iya ɗaukar nauyin aurar da su ga masu son su aure au.” Inji shi.
Ya ce sun yi murna da Sarkindaji ya ce zai ɗauki nauyin yi masu auren-gata. Saboda kowace sai da ta amince tukunna.
‘Ni Tausaya Wa ‘Yan Matan Na Yi, Ba Tilasta Su Ba’ -Sarkindaji:
“Ni fa na yi niyyar yin wannan ƙoƙarin saboda tausayawa ce ba don wani abu ba. Kuma babu wata ko guda ɗaya da aka ƙaƙaba wa wanda ba ta so.
“Mu mutanen karkara ne, Nnamani noma da aure shi ne abin damuwar mu. Kafin a fito da zancen auren sai da muka kafa kwamiti, kuma muka umarci kwamitin ya tuntubi dagatai da hakimai domin su tunruɓi iyayen yaran.
“Yaran nan kuma sai da aka tantance su. Daga mai shekaru 18 sai abin da ya yi sama zuwa 22. Wasu ma sun kai shekaru 23 zuwa masu 24.”
‘Yadda Al’ummar Jihar Neja Suka Goyi Bayan Auren-gatan ‘Yan Matan Mariga 100:
Al’umma daga cikin Jihar Neja sun nuna goyon bayan su kan wannan aure, kuma ba su ji daɗin dakatar da shirye-shirye da Ministar Harkokin Mata ta janyo aka yi ba.
Halima Sadiya ta ce, “A irin wannan mawuyacin hali da ake ciki, auras da ‘yan matan shi ne ya fi alfanu.”
Ta jinjina wa Gwamnan Neja, wanda ya yi niyyar tallafa wa kowace amarya da jarin Naira 100,000 domin ta yi sana’a.
Wani mai zaune a Minna, mai suna Gimba Evuti ya ce dukkan ‘yan matan sun isa aure, kuma da yardar su da amincewar su aka shirya yi masu auren. Kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja ya shirya tallafa masu. Wannan auren irin auren da aka yi ne na zawarawa a Kano. Hakan kuma ya na nesantar da yara daga aikata zinace-zinace.”
Ya ce ita Minista ba ta fahimci abin ba, saboda an sa kalmar marayu a batun. Amma ai ba abu ne da ya saɓa al’adun mu ba.”
Discussion about this post