Shugaban Cocin Angalika Henry Nsukuba, ya yi wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kukan yadda ‘raɗaɗin tsadar rayuwa, fatara, talauci da yunwa ke ci gaba da nuƙurƙusar talakawan Najeriya’.
Ya shaida wa Tinubu cewa “maganar gaskiya da rayuwa ta yi wa ‘yan Najeriya masifaffiyar tsada a cikin ƙasar nan.”
Daga nan sai ya yi kira da a gaggauta bijiro da hanyoyin sauƙaƙa rayuwar al’ummar ƙasar nan.
Limamin cocin ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke jawabi ga wakilan da suka halarci taro karo na biyu Cocin 12th Synod Diocese na Abuja, wanda aka gudanar a Ɗakin Bauta na Basilica of Grace, Gudu, Abuja, a ranar Asabar.
Kakakin Yaɗa Labaran taron, Folu Olamiti, ya ce Ndukaba ya bayyana musabbabin wasu matsalolin ga wasu tsirarun shugabanni, waɗanda “suka zame wa ƙasar nan gungun shaiɗanun da ba su ba a taɓa su a ƙasar nan.”
Ndukuba ya yi tsinkayen cewa “matsalar tsaron lafiya, rayuka da dukiyoyin jama’a ta kasance babbar cutar kansar da ke “zaizaye ƙasar nan.”
Ya ce ya na ganin cewa kamar Najeriya ta shiga sahun ƙasashen da numfashi kawai su ke yi, kafin su ƙarasa kai gargara irin su Somaliya da Sudan, waɗanda rikicin cikin gida ya cukurkuɗe su.
Ya danganta matsalar rashin tsaro a kan iyakoki, son ran shugabannin siyasa da shugabannin addinai, a matsayin masu ruruta wutar fitinar garkuwa da mutane, tare da haɗin-baki da jami’an tsaro, waɗanda ya ce su ke hana samun nasarar kakkaɓe matsalar ‘yan bindiga.
Ya nuna ɓacin rai ganin yadda tattalin arziki ya sukirkuce, ta yadda talakawa ne kaɗai ke ɗanɗana kuɗar wannan tsadar rayuwa da ake fama da ita a kowace rana.
Ya buga misali da cire tallafin fetur, tsada da ƙarancin fetur a halin yanzu, ƙarin kuɗin wutar lantarki, wanda ya ce sun jefa ‘yan Najeriya cikin tarangahuma.
Ya ce Cocin Angalika ya na goyon bayan Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa masu kakabin a samar wa ‘yan Najeriya sauƙin rayuwa kan batun ƙarin kuɗin wutar lantarki.
Ya ce akwai buƙatar a ƙara wa kowane ma’aikaci albashi a ƙasar nan, bisa la’akari da hauhawar farashin kayan masarufi da kayan abinci.
Discussion about this post