Mazauna jihar Sokoto da kewaye na fuskantar matsanancin karancin man fetur da ruwan sha a cikin yanayin zafi sama da digiri 42 a ma’aunin celcius.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa lamarin ya jefa mutane cikin mawuyacin hali a jihar.
NAN ta ruwaito cewa wasu ‘yan kasuwa da masu tuka babura da matafiya sun dakatar da sana’ar su saboda rashin man fetur. Wakilin NAN, wanda ya zazzagaya cikin carin Sokoto, ya ruwaito cewa mafi yawan gidajen man fetur ba su da shi.
Kadan daga cikin gidajen man da ke siyar da mai na siyar wa a tsakanin Naira 750 zuwa Naira 1,200 kowace lita, yayin da ‘yan bunburutu ke siyar wa kan Naira 2,000 a kowace lita.
Lamarin dai ya shafi zirga-zirgar ababen hawa inda kuɗin ababen hawa ya yi tashin Gwauron zaɓi ta yadda mutane ba su iya fita a wasu lokuttan.
Jarkar ruwa ya kai naira 120, sai da kuma ma’aikatar ruwa ta jihar ta na raba ruwa a tankuna ga al’umma a unguwanni.
Haka kuma ga rashin wuta da mutane ke fama da shi a jihar.
Discussion about this post