Uwar Ɗakin Fati mai zogale wacce mawaki Dauda Kahutu ya rangaɗa wa waka ta sallami ƴar aikinta, Fatima, wacce aka fi sani da Fati mai Zogale yanzu.
Kamar yadda Fati da faɗi a wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, ta ce wacce Uwar Ɗakinta ta sallameta bayan Rarara ya yi mata waka.
” Rarara ya zo wurin da muke siyar da zogale a Abuja ya siya zogale. Daga ganin sa sai na kiɗime na ce yau gani ga Rarara, ya siya Zogale ya kuma tambayi suna na, suka tafi.
“Bayan haka kawai sai naji waka ta karaɗe gari wai ai ni ce Rarara ya yi wa waka. Fati mai Zogale.
” Daga nan sai wacce na ke wa aiki ta ce ita ce mai wuri, ba a yi mata waka ba sai ni ɗanwake a Otel, ban isa, ta fatattake ta ce in bar mata wurin siyar da Zogalenta.
Sai dai bayan haka uwar ɗakin Fati Mai zogale ta wata kila bayan ta yi tunani, ta fito ta na karyata xewa wai ta kori Fati Mai Zogale.
“Sai dai Fatin ta ce shirga karya ta yi, ba yanzu ba ta taba korar ta bayan sun ɗan samu saɓani wurin siyar da Zogale.
Wakar Fatinmai Zogale dai ya karaɗe shafukan sada zumunta da wasu gdajen radiyo inda ake saka wa ana ji don nishaɗi.
Discussion about this post