Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas, ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nysome Wike, ya sauka mulki ba tare da kulawa da matsalolin da ke tattare da ɓangaren kiwon lafiya ba.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Fubara, Nelson Chukwudi ya fitar, ya ce Gwamna Fubara ya ce Cibiyoyin Kula la Lafiya a jihar Ribas sun yi ƙaranci sosai, saboda gwamnatin Wike ba ta inganta ƙanana da manyan asibitocin jihar ya bar su babu kulawa ko kaɗan.
Ya ce manyan asibitocin jihar biyu ne kaɗai ke aiki. “Daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ribas sai kuma na Jami’an Fatakwal.”
Ya ce zai yi gagarimin gyara a manyan asibitocin shiyya biyar a faɗin Jihar Ribas, domin a rage cinkoson marasa lafiya a asibitoci biyu na koyarwar da ke aiki yanzu a jihar.
Ya ƙara da cewa zai farfaɗo da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko da na mataki na biyu.
Da Fubara ya koma kan halin da makarantun jihar ke ciki, ya ce Wike ya ‘ya bar kashi 75% na makarantun Ribas babu malamai, kashi 90 na gine-ginen makarantun a lalace suke’.
Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas, ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Ribas wanda ya gada, Nysome Wike ya tafi ya bar makarantun jihar a lalace, kuma babu malamai wadatattu da ingantattu.
Ya ce ya gano haka ta hanyar ɗaukar hayar wani kamfanin da ya bibiyi gaba ɗaya makarantun jihar.
Fubara ya ce kamfanin mai suna New Global, ya bayyana buƙatar sa wajen haɗa kai da Gwamnatin Jihar Ribas domin ƙara yawan malaman makaranta nagartattu.
Fubara ya ce tashin farko ya fara umartar kamfanin ya gano halin da makarantun jihar suke ciki baki ɗayan su.
Ya ce ya yi hakan ne a lokacin da kamfanin mai suna New Global ya nuna cewa zai zuba Dala miliyan 5 wajen inganta ilmi ta hanyar samar da kwamfitoci da sauran kayan inganta koyon darussa a zamanance a makarantun firamare.
“Bayan kamfanin ya kewaya faɗin jihar ya ga halin da makarantun ke ciki, za ka yi mamakin jin cewa kashi 75 bisa 100 na makarantun ba su da malamai. Kuma kashi 90 bisa 100 na ɗaukacin makarantun jihar, duk gine-ginen su a lalace suke.
“To a irin wannan ya za ka saka Dala miliyan 5 a cikin makarantun da ke fama da rashin malamai kuma gine-ginen su duk su na a lalace?”
Ya ce gwamnatin sa za ta bai wa ilmin firamare muhimmanci, domin daga matakin firamare ake fara gina matasan da a gobe su ne za su zama shugabanni.” Inji Fubara.
Discussion about this post