Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Abdullahi Ganduje, ya gargaɗi gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da ya daina amfani da dabarun raba kan jama’a wajen fakewa da gazawar sa ga al’ummar jihar.
Kakakin Ganduje, Edwin Olofu ya bayyana a wata sanarwa da ga Ganduje cewa ɓaɓatu kawai gwamna Yusuf yake yi saboda ya gaza nuna wani abu da ya yi a Kano tun bayan ɗarewar sa kujerar gwamnan jihar, duk da dimbin kuɗin da ake dankara wa Kano daga Abuja.
Ganduje na mayar da martani ne kan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da karbar cin hancin dala 413,000, da kuma Naira biliyan 1.38.
” Maimakon gwamnatin Kano ta maida hankali wajen tabbatar da samun wadata da walwalar jama’a sun karkata ne wajen fallasa zargin abin da basu da iko akan sa.
” Saboda rashin sani da karancin Ilimi da ya dabaibaye Abba da maƙarrabansa, sun manta cewa akwai umarnin kotun tarayya da ta ce wannan batu na cin hanci ba ya karkashin jiha, shari’a ce ta gwamnatin tarayya.
” Amma za su iya komawa su gyara kurakuransu ta hanyar bin turakun da muka daddasa su yi koyi da yadda muka yi ayyukan mu a baya.
A karshe ya ce zai fi dacewa innda gaske ne gwamnati ke yi, ta faro bincikenta tun daga 1999 ne, idan da gaske babu lauje cikin naɗi.
Discussion about this post