Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kama wani ƙasurgumin mai safarar makamai mai suna Mansir Muhammed a tashar mota a garin Jalingo, Jihar Taraba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Onyema Nwachukwu ya sanar da haka ranar Litini a Abuja.
Nwachukwu ya ce sojojin sun kama Muhammed da bindiga kirar ‘Semi-Automatic Pump-action’, bindiga kirar hannu daya, mota kirar Peugeot, wayoyin hannu biyar da naira 45,000.
Ya kuma ce Muhammed ya bai wa jami’an tsaron bayanan da ya taimaka wajen kamo sauran abokan aikinsa da suke siyar wa mahara makamai.
Bayan haka Nwachukwu ya ce dakaru sun kuma dakike wani harin yin garkuwa da mutane a garin Zaki-Biam dake karamar hukumar Zaki-Biam a jihar Benuwe.
“Jami’an tsaron sun kashe daya daga cikin maharan sannan suka kwato bindiga daya kirar Beretta Pistol da harsasai 9.
Daga nan dakarun sun kama wasu mutane biyu da makamai a babur a kauyen Miyande dake karamar hukumar Takum.
Sannan kuma sojoji sun kama wani mutane da bindiga kirar AK-47 daya, bindiga kirar automatic rifle, harsasai biyar da babur daya.
Nwachukwu ya ce rundunar za ta ci gaba da kokari wajen samar da tsaro sannan ya yi kira ga mutane da su ci gaba da basu hadin kai wajen fallasa ƴan bindiga da ayyukan su a ko ina a fadin kasar nan.
Discussion about this post