Garkuwa da ɗaliban sakandare ‘yan mata na garin Chibok a ranar 14 ga Afrilu, 2014 ya saka sunan Najeriya ya fito a sahun ƙasashen da suka yi ƙaurin suna a ta’addanci a faɗin duniya.
Boko Haram da a farko aka riƙa yi wa kallon wasu ‘yan buyagi, cikin ƙanƙanen lokaci suka buwayi Najeriya, suka kuma yi suna da shahara a duniya.
Yau shekaru goma kenan tun bayan da ɗaliban Chibok suka faɗa hannun Boko Haram, kuma har yau ana neman 91 daga cikin su, ba amo ba labari.
Kuma wannan batutuwa da har yanzu ake kwana da tashi da su, yau sun zama ruwan dare, ko’ina garkuwa da mutane ta zama babban bala’i.
Boko Haram sun kai hari sakandaren kwana ta ɗalibai mata, GGSS Chibok, Jihar Barno, a ranar 14 ga Afrilu, 2014, suka arce da ‘yan mata 276.
An loda ɗaliban cikin buɗaɗɗun motoci da jijjifin asubahi, aka nausa da su cikin Dajin Sambisa.
Guda 57 daga cikin ɗaliban sun riƙa dirowa ƙasa, suka tsere, suka koma gida.
Tsakanin 2016 da 2023, guda 21 sun tsere daga hannun Boko Haram, bayan an yi masu auren-dole da ‘yan ta’adda.
Waɗanda suka kuɓuta daga hannun Boko Haram, sun koma gida ɗauke da ‘ya’ya 34, kama daga ɗan watanni 5 zuwa masu shekaru 7 a duniya.
Wasu daga cikin matan da suka kuɓuta, sun koma daji wurin mazan na su ‘yan Boko Haram.
Ɗaya daga cikin ‘yan mata 57 ɗin da suka diro daga cikin motocin da suka ɗauke su, an kai ta yi Digiri a wata Kwalejin Amurka.
Adadin waɗanda aka ceto ko suka tsere daga hannun Boko Haram, sun kai 128. An riƙa kuɓutar da su ne kashi-kashi, ba a lokaci ɗaya ba.
Har yanzu ana neman guda 9, waɗanda babu labarin su. Sai dai iyayen su na sa ran za su iya dawowa. Wasu kuma sun haƙura, sun ƙaddara mutuwa ta ɗauki yaran na su.
Boko Haram sun ɗaura wa Falmata Yama auren-dole. Bayan shekara biyar ta haifi mace, mai suna Jinƙai (God’s Grace). Bayan shekara 8 a hannun Boko Haram, Falmata ta koma gida da yara uku, a ranar 7 ga Satumba, 2023. An ceto ta tare da wasu ɗalibai biyu.
Mijin Falmata yanzu haka tubabben ɗan Boko Haram ne, su na zaune cikin Maiduguri.
Aisha Grema da Mary Dauda su na son mazan su, bayan mazan sun tuba daga Boko Haram.
Amina Nkeki ce ɗaliba ta farko da ta fara kuɓuta daga hannun Boko Haram, ita ce Amina Nkeki.
Mijin Amina mai suna Mohammed Hayatu, ya tuna daga Boko Haram, shi da wasu mazan ɗaliban ɗaliban na Chibok.
Yanzu haka Amina ta na karatun digiri a Jami’ar Amirka da ke Adamawa, kuma Gwamnati ke ɗaukar nauyin karatun ta.
Cikin watan Mayu, 2016 an karɓo ɗalibai 21, bayan gwamnatin Swiss da Red Cross ta Duniya sun shiga tsakani, an yi musayar bursunonin yaƙi tsakanin Gwamnatin Najeriya da Boko Haram.
Cikin watan Mayu, 2017 an karɓo wasu ɗalibai 82 daga hannun Boko Haram, bayan tattauna musayar fursunoni.
Wannan sace ɗaliban ce ta buɗe ƙofa ga ‘yan bindiga da ke addabar Arewa maso Yamma, su ma suka maida hankali kan sata ko yin garkuwa da ɗaruruwan ɗalibai, domin neman biyan wata buƙata a hannun gwamnati.
Yayin da aka cika shekara 10 bayan sace ɗaliban Chibok, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce har yanzu ba za su yi ƙasa a guiwa ba, sai sun ga sauran ɗalibai 91 da ba a jin ɗuriyar su sun koma hannun iyayen su.
Tsohon Gwamnan Barno Kashim Shettima, wanda a zamanin sa ne aka sace ɗaliban, shi ne Mataimakin Shugaban Ƙasa a yanzu.
Yayin da kisan 50 daga cikin iyayen ɗaliban Chibok sun mutu saboda takaicin jiran dawowar ‘ya’yan su, PREMIUM TIMES na kira cewa kada a manta da sauran ɗaliban Chibok 91 da har yau ke hannun Boko Haram.
Sannan kuma tilas Gwamnatin Tarayya ta miƙe tsaye wajen daƙile garkuwa da ɗalibai da ya zama ruwan dare yanzu a makarantun Arewa maso Gabas da kuma garkuwa da sauran mutanen gari.
Yaƙi da ta’addanci abu ne da ya kamata a bai wa muhimmanci sosai. Sai an kawar za zargin harƙallar kuɗaɗe a yaƙin, kuma ya kasance ƙananan sojojin da ake turawa bakin daga, su da iyalan su na samun kyakkyawar kulawa, ba wai a riƙa yi masu turin-je-ka-ka-mutu ba.
Discussion about this post