Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, Nysome Wike, kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, ya bayyana cewa shi da tsohon ubangidan sa, kuma tsohon Gwamnan Ribas, Peter Odili, ba su jituwa.
Odili wanda ya taɓa yin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, ya yi gwamnan Ribas daga 1999 zuwa 2007. Rotimi Amaechi ne ya gaje shi, daga 2007 zuwa 2015, inda daga nan kuma Wike ya zama gwamna daga 2015 zuwa 2023.
Dukkan tsoffin gwamnonin dai sun yi mulki ne a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
A tattaunawar da aka yi da Wike ranar Talata a Abuja, a gidan talabijin na Channels, Wike ya ce: “A yau ɗin nan dai a siyasance, ni da Odili ba mu jituwa. Ba ma tafiya tare. Saboda dukkan mu kowa na da bambancin ra’ayin siyasar sa.”
“A ɓangare na dai ni mun raba hanya da shi. Girkin da muka ɗora a baya tare, an sauke, an kwashe, an cinye, kowa ya kama gaban sa.
“Kuma ko a nan gaba ba zai kasance mu sake shan inuwar siyasa ɗaya ba. A’a, kowa ya kama gaban sa.”
Wike ya kuma ragargaji mambobin majalisar kamfen ɗin shugaban ƙasa ta PDP a Jihar Ribas, wadda ta ƙunshi har da su tsohon Ministan Sufuri, Abiye Sekibo, tsohon Shugaban PDP na Ƙasa, Uche Secondus da sauran su.
A makon jiya ne dai kwamitin suka nuna goyon bayan su ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu. Amma kuma sun goyi bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, suka ƙi goyon bayan Wike a kan saɓanin siyasar sa da Gwamna Fubara.
Kwamitin na PDP na Jihar Ribas sun kuma caccaki Wike dangane da cin zarafin da Wike ɗin ya yi wa Odili, wanda suka kira jagoran tafiyar siyasar su.
A ranar Talata ce Wike ya kira su “tsoffin kwanduna da ko shara ba a iya zubawa a ciki. Kuma ba su da wani tasiri a siyasa,” ya ce shi ne ya fatattake su daga cikin jam’iyya.
Lokacin da Wike ya na gwamna, ya sha yin jinjina da yabo da Odili da matar sa Mary, tsohuwar Mai Shari’a a Kotun Ƙoli, saboda su biyun sun taimaki matar Wike ɗin ita ma ta zama mai shari’a.
A wani tsohon bidiyo, an taɓa nuno Wike ya na cewa ba zai taɓa yin watsi da Peter Odili ba. Ya ce da ya watsar da Odili, gara ya watsar da takarar sa ta neman zama shugaban ƙasa.
“Kada Allah ya sa na yi ƙarkon da za a wayi gari wata rana na yi abin da na sa Dakta Odili da iyalin sa kuka. Saboda Odili da matar sa sun sha tsangwama da sharri da tuggu, saboda kawai sun taimaka wa mutane iri na.”
Wuraren taruka da dama Wike ya sha nuna cewa a tarihin siyasar Ribas ba a taɓa yin gwarzo kamar Odili ba.
Har Cibiyar Nazarin Aikin Shari’a Wike ya gina lokacin da ya na Gwamnan Ribas, ya raɗa wa cibiyar sunan Mary, matar Odili.
Rikicin Odili Da Wike:
Tsohon Kwamishinan Ruwa na Jihar Ribas, David Briggs, a wani bidiyo da ya watsa, a shafin sa na Facebook, ya bayyana kalaman cin zarafin da Wike ya yi wa Odili da cewa, “rashin mutunci ne.”
Briggs ya ce Wike na jin haushin Odili saboda ya ƙi bayar da goyon baya a tsige Gwamna Fubara, wanda a yanzu ba ya ga-maciji da Wike.
Rikicin Wike Da Fubara:
Wike ya taimaki Fubara ya gaje shi ya zama Gwamnan Ribas a zaɓen 2023. Amma sun raba hanya saboda Wike ya nemi ya maida ‘yan siyasar jihar Ribas da Gwamna Fubara da gwamnatin jihar cikin aljihun sa, shi kuma Fubara ya ƙi amincewa.
Discussion about this post