Darajar Naira na ci gaba da farfaɗowa, yayin da aka yi hada-hadar Dala daga Naira 1,311 da Naira 1,200 a farashin masu zuba jari da kuma masu fitar da kaya ƙasashen waje.
A farashin gwamnati na bankuna dai an sayar da kowace dala ɗaya kan Naira 1,278 a ranar Talata.
Bayanai daga shafin yanar gizo na FMDQ ya nuna cewa darajar Naira ta ƙaru da Naira 30.92 a ranar Talata, idan aka kwatanta da ranar Alhamis ta makon jiya, wato ranar 28 ga Maris, kafin Easter, inda aka sayar da Dala 1 kan Naira 2,309.39.
Darajar Naira A Makon Jiya:
Naira na ci gaba da ƙoƙarin kuɓuta daga kamun-kazar-kukun da Dala ta yi mata.
Naira ta fara ƙwatar wa kan ta martaba da daraja daga hannun Dala, yayin da aka sayar da ita Dala 1 kan Naira 1,382.95 a farashin gwamnati, a ranar Talata ta makon jiya.
Kafin sannan dai ana sayar da Dala 2 Naira 1,408 ne a ranar Litinin ta makon jiya.
Amma kuma hada-hadar masu zuba jari da masu fitar da kaya ƙasashen waje, an yi musayar Dala kan Naira 1,300 zuwa 1,489.
Idan ba a manta ba dai a ranar Talata ce ta makin jiya Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙara wa masu karɓar lamuni a bankuna kuɗin ruwa, daga kashi 22.75 zuwa kashi 24.75.
Tun a ranar Juma’a ne dai Naira ta fara shaƙar numfashi, bayan Dala ta yi mata cin-kwalar-kuturun da ta sumar da ita.
Rahoton da wannan jarida ta buga a ranar Asabar, ya nuna yadda darajar Naira ta ɗan ɗaga sama inda a ranar Juma’a aka sayar da Dala 1 kan Naira 1,431.49.
Bayanan da suka fito daga Sashen Hada-hadar Kuɗaɗen Waje, sun nuna cewa darajar Naira ta ɗaga da ƙarfin Naira 21.79, wato ta ƙaru da kashi 1.5, idan aka kwatanta yadda aka sayar da Dala 1 kan Naira 1,453.28 kafin ranar Juma’a.
Amma a ɓangaren musayar kuɗaɗe ga masu zuba jari da masu fitar da kaya wajen Najeriya, an yi hada-hadar Dala kan Naira 1,468 da kuma 1,301.
Wannan jarida ta buga labarin cewa CBN ya raba Dalolin da ake bin sa bashin karɓa, ya ƙara yawan gejin kuɗaɗen asusun kuɗaɗen waje.
Babban Bankin Najeriya ya bayyana cewa babu sauran wani ko wasu masu bin sa bashin karɓar kuɗaɗen wajen da suke jiran karɓa, domin yin hada-hadar da Gwamnatin Najeriya ta amince su yi da kuɗaɗen.
Wannan yunƙuri da kuma ƙoƙari da dai Kakakin Yaɗa Labaran CBN ce, Hakama Sidi-Ali ta bayyana shi.
Hakama ta ce wannan wani hoɓɓasa ne domin ɗaukar ƙaƙƙarfan matakin dawo da martaba da ingancin tattalin arzikin ƙasa.
A cewar ta, “CBN ya kammala biyan Dala biliyan 1.5, wato kenan ya gama biyan sauran balas da kwastomomin sa masu buƙatar kuɗaɗen ƙasashen waje ke bin sa.
Ta ƙara da cewa sai da aka yi bin-diddigi, tankaɗe da rairaya wajen tantance waɗanda ƙa’idar doka ta nuna sun cancanta a ba su kuɗaɗen na ƙasashen waje.
Hakama ta ce kamfanin bin-diddigin kuɗaɗe mai zaman kan sa mai suna Deloitte Consulting aka ɗauko hayar aikin tantancewar, inda aka zubar da duk waɗanda ba su cancanci a ba su canjin kuɗaɗen na waje ba.
“Duk wani bayanin hada-hadar da ke da alamar tambaya, sai a hana shi kuɗin, a ajiye fayil gefe, a ce za a ci gaba da bincike.” Cewar ta.
Sannan kuma Hakama ta ce CBN ya ƙara yawan kuɗaɗen waje a cikin asusun Najeriya daga ranar 7 ga Maris, inda ya zuwa ranar akwai Dala biliyan 34.11 a cikin asusun, adadin da rabon da a samu yawan haka tun bayan watanni takwas baya.
Dangane da wannan biyan kuɗaɗen da CBN ta yi, ɗan jarida kuma mai sharhin yau da kullum, Aliyu Ɗahiru-Aliyu, wa wallafa a shafin sa na Facebook cewa:
“Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa ya yi “clearing FX backlog” da hakan yake nufin an biya bashin duk wata buƙatar Dalar Amurka da aka nema daga gurin sa. Hakan daidai yake da a ce kamar ana bin ka bashi, kuma ka na da buƙatar kuɗi, sai ka biya bashin da ake bin ka. Ka ga za ka samu kuɗi da yawa a hannun ka kenan.
“Biyan bashin buƙatar Dala daga hannun CBN kuwa zai bayu ga wadatuwar Dala a hannun ‘yan kasuwa, musamman tun da CBN ɗin ya fara ba su dalar a ƙaramin farashi, kuma ya ce kada ‘yan canji (BDC) su ci ribar da ta wuce kaso 1 cikin 100.”
Ya ce idaan Dala ta wadata a kasuwa, to farashin ta zai sauko. Idan farashinta ya sauko to kayan da ake siyowa daga waje za su yi sauƙi, don haka sai farashin kayayyaki ya sauka a kasuwa.
“Ina zaton saukar da dalar take yanzu ya na da alaƙa da wannan labari. Masu riƙe da Dala sun sani cewar kwanan nan za ta yi yawa tun da CBN ya gama biyan bashi. Don haka suka fito da wacce suka ɓoye, suka fara sayarwa. Wannan shi ne ya janyo a karon farko a Najeriya aka samu farashin Dala a kasuwa ya yi ƙasa da farashin ta har a gurin gwamnati.”
Discussion about this post