Hukumar gudanar da bincike kan yakar cutar daji ta kasa NICRAT Usman Aliyu ya bayyana wasu matsalolin da hukumar ke fama da su wajen kawo karshen fama da cutar.
Aliyu ya ce rashin isassun ma’aikatan jinya, rashin ware isassun kudade domin yakar cutar da rashin yi wa mutane allurar rigakafin cutar na daga cikin matsalolin da ake fama da su.
Shugaban NICRAT ya fadi haka ne a taron wayar da kan ‘yan jarida da mahimmiyar rawar da hukumar ke takawa wajen yaki da cutar a Najeriya.
Matsalolin dun haɗa da
Rashin ware isassun kudade
Aliyu ya ce har yanzu gwamnati ba ta iya samar da kudade isassu ba a kasafin kudin kasa domin wannan aiki. Hakan ya sa muna samun cikas wajen aiwatar da ayyukan mu.
Rashin yin allurar rigakafin cutar
Shugaban fannin dakile yaduwar cutar ta hukumar Usman Waziri ya ce kasashen da suka ci gaba na yi wa maza da mata allurar rigakafin cutar domin samar musu kariya daga kamuwa da cutar bayan sun girma.
Ya ce sai dai a Najeriya saboda tsadar maganin yin allurar rigakafin ya sa ake yi wa mata kadai allurar rigakafin sannan ko a hakan ma ba duka ‘yan Najeriya ne suka amince da yin allurar rigakafin ba.
Karancin ma’aikatan jinya
Wata ma’aikaciyar lafiya dake aiki da asibitin kula da masu fama da Daji ‘Stephen James ‘ a kasar UK Ayodelle Obaro ta ce kamata ya yi a samu isassun ma’aikatan jinya a fannin kula da masu fama da cutar.
Obaro ta ce tausayi, samun ilimin kula da masu fama da cutar da kiyaye sharuddan kula da masu fama da cutar na daga cikin ilimin da ya kamata ma’aikatan jinya na da shi kafin su fara aikin kula da masu cutar.
Cutar Daji a Najeriya
Sakamakon binciken da ‘Global Cancer Observatory (GLOBOCAN) ya gabatar ya nuna cewa mutum 120,000 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 80,000 a Najeriya a shekarar 2022.
Aliyu ya ce nau’ikan cutar dake yaduwa a Najeriya sun hada cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina kashi 14.1%, dajin dake kama nono kashi 24.3%, dajin dajin dake kama gaban mace 10.7%, dajin dake kama dubura 6.4%, dajin dake kama makogwaro 4.1%.
Discussion about this post