Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya ya bai wa Hukumar EFCC damar kulle asusun banki 1,146, mallakar wasu ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, waɗanda hukumar ke binciken su kan laifukan hada-hadar kuɗaɗen waje ba bisa ƙa’ida ba, harƙallar karkatar da kuɗaɗe da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci.
Mai Shari’a ya bayar da umarnin cewa EFCC ta riƙe tare da kulle asusun bankin su, “har zuwa ranar da za a kammala bincike.”
Mai Shari’a Ewete ya bada hukuncin ne lokacin da yake duba buƙatar lauyan EFCC, Ekele Iheanacho, ya ce: “wannan kotu ta bai wa EFCC damar kulle asusun bankin mutanen da ta ke bincike da aka lissafo wa kotun, waɗanda ake zargi da hada-hadar kuɗaɗen waje ba bisa ƙa’ida ba, karkatar da kuɗaɗe da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci.
“Dukkan asusun na su za su ci gaba da kasancewa a kulle, har zuwa nan da kwanaki 90 ɗin da za a shafe ana binciken.”
Mai Shari’a ya ci gaba da cewa: “Binciken farko-farko ya nuna cewa asusun bankunan har 1,146 na da alaƙa da masu hada-hadar kuɗaɗen ‘kirifto’, su na ɗaga farashin kuɗaɗen waje, tare da karya darajar Naira, kuma su na karkatar da kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya.”
Mai Shari’a ya ce don haka akwai buƙatar EFCC ta kulle asusun bankunan mutanen har zuwa kammala bincike da kuma gurfanar da waɗanda aka samu da laifi.
An ɗage shari’ar zuwa ranar 23 ga Yuli, 2024.
Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar 29 ga Afrilu cewa, kamfanonin da lamarin ya shafa, sun haɗa da na ɗaiɗaikun mutane, kamfanonin harkokin ayyukan noma, ƙananan bankunan kasuwanci, na ayyukan injiniya da sauran su.
Discussion about this post