Iran ta gargaɗi Isra’ila kada ta kuskura ta ce za ta kai harin ramuwar gayya kan kasar Iran bayan harin rokoki da ta kai mata ranar Asabar.
Bayan haka Iran ta ce ta kammala hare-haren da ta kaddamar akan Isra’ila a yau domin maida mata da martanin harin da ta kai mata a ranar 1 ga Afrilu.
Iran ta kaddamar da hare-hare kan Isra’ila ta hanyar amfani makaman roka da kuma jirage marasa matuka ranar Asabar.
Iran ta bayyana wannan hari a matsayin ramuwar gayya ga harin da Iran ta kai mata a farkon Adrilu.
Tun bayan harin da Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran a Syria ranar daya ga watan Afrilu aka shiga fargabar yiwuwar barkewar rikici tsakanin kasashen biyu
Wanna. Hari na ɗaya ga Afrilu ta yi sanadiyyar kashe Dakarun Iran da suka haɗa da janar-janar biyu da kuma wasu ‘yan kasar mutum shida.
Tun a wancan lokaci ne Iran ta yi gargadin cewa za ta maida wa Isra’ila martani ba da dadewa ba.
Sai dai kuma bayan harin Firaiminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi wa al’ummar kasarsa jawabi yana mai cewa dakarun Isra’ila “a shirye suke ko mai ta fanjama fanjam.”
Bayan haka kuma tarayyar Turai da Burtaniya sun yi tir da wannan hari da Iran ta kai kasar Isra’ila suna masu cewa suna tare da Isra’ila komai rintsi.
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya bayyana cewa Iran ta tafka ganganci harin martani da ta kai Isra’ila.
Ya ƙara da cewa Birtaniya da kasashen da ke ƙawance da Isra’ila za du bi abin sannu a hankali domin gujewa ɓarkewar rikici mai tsanani tsakanin kasashen biyu.
Discussion about this post