Fitaccen fasto mai tashe a soshiyal midiya, Jerry Eze, zai haɗa gangamin yin azumi da addu’o’in kwanaki huɗu, domin hana mutuwa sake ratsawa cikin ‘yan fim ɗin kudu, waɗanda aka fi sanin farfajiyar su da suna Nollywood.
Shugaban Ƙungiyar Jaruman Nollywood, Emeka Rollas ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata.
Eze wanda shi ke da Cocin Addu’o’i na NSPPD, coci ne na yanar gizo da ake komai ta online.
Rollas ya ce za a yi gangamin addu’o’in biyo bayan rasuwar wasu jarumai biyu a hatsarin kwale-kwale da ya ritsa da su a wani wurin ɗaukar fim, tare da masu ɗaukar fim ɗin su biyar, ciki har da Jnr Pope a Asaba.
A kan haka ne Ƙungiyar Jaruman Nollywood suka yanke shawarar yin azumi da addu’o’in neman hana mutuwa ratsawa a cikin masana’antar su.
Wasu jaruman Nollywood da suka mutu a watannin baya, sai kuma na baya-bayan nan sun haifar da damuwa sosai a cikin Nollywood.
Daga cikin waɗanda aka rasa akwai Mista Ibu wanda ya mutu ranar 2 ga Maris, 2024, bayan an yi masa tiyatar guntile masa ƙafa.
Sai ranar 25 ga Maris, 2024 kuma aka tashi da rasuwar Amaechi Muonagor, watanni uku bayan an gano ya na fama da cutar ƙoda da kuma ciwon diyabitis da shanyewar ɓarin jiki.
Rollas ya ce za su yi taron gangamin addu’o’in daga ranakun 2 ga Mayu zuwa 5 ga Mayu, 2024, tsakanin ƙarfe 6 na safe da ƙarfe 1 na ranar Lahadi a Streams of Joy, Abuja, a Dandalin Taro na M&M, ƙarfe 11 na rana.
Discussion about this post