Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa tsakanin Janairu zuwa Maris na 2024 ɗin nan ta kashe ‘yan ta’adda 2,352, sannan kuma ta kama wasu 2,308, tare da ceto mutum 1,241 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake ƙarin haske dangane da ayyukan sojojin a faɗin ƙasar nan.
Ya ce daga cikin kwamandojin ‘yan ta’adda da aka samu nasarar bindigewa, akwai Abu Bilal Minuki, Shugaban ‘yan ta’addar Is-Al Firqan da ke Gundumar ISGS da ISWAP, sai kuma Haruna Isa Boderi.
Buba ya ƙara da cewa wasu daga cikin ‘yan bindigar da ke ta’addanci a dazukan Birnin Gwari, Jihar Kaduna da kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, duk an aika da su barzahu a ranar 21 ga Fabrairu.
Ya lissafa gogarma-gogarman da aka kashe har da Kachallah Damina, wanda aka bindige a cikin Maris, tare da wasu zaratan sa fiye da 50, har da Kachallah Alhaji Ali, Kachallah Idi (Namaidaro), Kachallah Kabiru (Doka), Kachallah Azarailu (Farin Ruwa), Kachallah Balejo, Kachallah Ubangida da Alhaji Baldu.
Buba ya ce an samu wannan gagarimar kakkaɓe dandazon ‘yan ta’adda ta hanyar farmakin haɗin-guiwa da sojojin ƙasa da na sama a sansanonin ‘yan ta’addar.
Ya ce an samu bindigogi 2,847, harsasai 58,492, yayin da aka hana ɓarayin mai arcewa da mai na sama da Naira biliyan 20 a cikin watanni ukun.
Discussion about this post