Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya gargadi Bello El-Rufai, dan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya guji yi wa Majalisar barazana kan binciken da ta ke yi kan gwamnatin mahaifinsa na tsawon shekaru takwas.
Liman ya ce Bello ya aika masa da sakonnin batanci da yawa a matsayinsa na Shugaban Majalisar Dokokin Jihar ta WhatsApp, dangane da binciken mahaifinsa.
Kakakin majalisar ya kuma yi karin haske kan cewa Bello ya yi masa rashin mutunci a shafukan sada zumuntan sa, ciki har da wasu sakonni guda biyu a shafinsa na twitter da suka yi kira da cewa Idan faɗa za a yi a shirye yake a haɗu a filin daga’ da kuma rashin mutunta dukkan mambobin majalisar.
Liman ya ce hakan da Bello ya yi ba zai hana majalisar binciken gwamnatin mahaifinsa ba da irin badaƙalar da ya aikata a lokacin mulkin sa.
Bello El-Rufai ne ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayya wanda shiyyar sa ya haɗa da gundumar Makera inda Kakakin Majalisar jihar ya ke wakilta a Kaduna.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda tsohon kakakin majalisar Yusuf Zailani ya shima ya zame kansa daga badakalar ciwo bashin dala miliyan 350 a lokacin gwamnatin El-Rufai.
Ya ce tsohon gwamnan ya yi gaban kan sa ne wajen amso bashin da raba wa na kusa da shi kwangilolin da ake zargin an yi su a jihar.
Discussion about this post