Wata mata da ba a san ko ita wacece ba ta kashe kanta a jihar Enugu.
Matar ta kashe kanta bayan ta shiga ofishin ‘yansandan dake Ogui a karamar hukumar Enugu ta Arewa ta ajiye ‘ya’yanta uku a ofishin sannan ta ruga a guje ta fada titi mota ya bankade ta nan take ta yi sallama da duniya.
Wasu mutane sun ce matar sai da ta yi wa kanta zindir kafin ta afka kan titin.
Babba daga cikin ‘ya’yanta na da shekaru shida sai kuma mai shekara 4 da 2.
Wannan abin takaicin dai ya faru a karshen makon jiya.
Wasu ‘yansanda da masu shaguna dake kusa da ofishin jami’an tsaron sun zargi tsananin talauci ne yasa matar ta kashe kanta.
Wasu mutane sun ce a kwanakin baya mijin matan ya gudu ya barta da ‘ya’yan da ake zaton shine dalilin da ya sa ta kashe kanta.
Daya daga cikin yaran bayan an tambaya ta inda mahaifin su yake ta ce ya bace.
Discussion about this post