Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi kira ga Majalisar Tarayya cewa su rage yawan kiran ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya zuwa Majalisa, da sunan kare kan su gaban kwamitin bincike.
Da ya ke magana lokacin da Kakakin Majalisar Tarayya, Tajuddeen Abbas da shugabannin majalisa suka kai masa ziyarar buɗe-baki a ranar Laraba, shugaba Tinubu ya ce yayin da neman ba’asi da sa-idon da majalisa ke wa ma’aikatun gwamnatin tarayya na da muhimmanci sosai, ta hanyar tabbatar da bin doka da ayyukan bisa ƙa’ida, to amma kuma yawan kiran manyan jami’an gwamnati zuwa majalisa zai hargitsa ayyukan da suke yi da kuma kawo cikas ga gudanar da ayyukan da aka ɗora masu su kammala cikin lokaci, domin amfanar al’umma baki ɗaya.
Daga nan ya yi kira ga ‘yan majalisa su rage yawan harankazamar kiran manyan jami’an gwamnati, so riƙa tafiyar da lamarin a hankali.
“Ina yawan kallon yadda ake zaman kwamitoci daban-daban, inda ake kiran ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya, domin su bada wani ba’asi kan wani bincike. Na yi wa Kakakin Majalisar Tarayya ƙorafin cewa su bar talaka ya sakata ya wala. A ƙyale jami’an nan su yi aikin su. Ba mu ce wai ba ki da wani tasiri ba. Kuma ba cewa muke yi kada ku yi aikin da doka ta wajibta maku ba. Amma dai a riƙa sara ana duban bakin gatari, a ƙyale jami’an nan su yi aikin su.” Cewar sa.
Ire-iren Gayyatar Da Tinubu Ya Ce A Daina:
Majalisa na neman Dala miliyan 300 a hannun masu lafiyar Ma’aikatar Kula da Lafiya ta Ƙasa:
Kwamitin Majalisar Tarayya Mai Lura da Ayyukan Ƙanjamau, Tarin Tibi, Zazzabin Maleriya ya na neman yadda aka yi da Dala miliyan 300, wadda aka ciwo bashi cikin 2018, da nufin ayyukan daƙile cutar zazzaɓin cizon sauro.
Wasan ɓuya da zilliyar manyan jami’an Ma’aikatar Lafiya wajen kasa yi wa kwamiti bayani ya sa kwamitin ya gayyaci Ministan Harkokin Lafiya, Muhammad Pate, domin ya yi ƙarin bayani.
Ba dai a lokacin Minista Pate aka karɓo bashin ba. Pate na cikin ministocin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa cikin Agusta, 2023.
Kwamitin Majalisa ya aika wa Minista Pate sammacin kiran gaggawa a ranar Talata yayin zaman sauraren yadda aka kashe kuɗaɗen, bayan Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Lafiya, Daju Kachollom ya kasa bayyana a gaban kwamitin, domin ya yi bayani.
Cikin 2018 ne dai a zamanin mulkin Buhari, Gwamnatin Najeriya ta ciwo bashin Dala miliyan 300 daga Bankin Duniya, Bankin Musulunci da AfDB domin shirin kakkaɓe zazzaɓin cizon sauro a Najeriya.
Sai dai kuma Majalisar Tarayya na zargin cewa maimakon a yi amfani da kuɗaɗen wajen kakkaɓe sauro da zazzaɓin cizon sauro, wasu masu cikakkar lafiya sun kakkaɓe kuɗaɗen ƙarƙaf.
Ganin yadda Kachollom ya kasa bayyana, sai kwamitin ya gayyaci Ministan Lafiya Pate, domin ya bayyana a cikin sa’o’i 72 ko kuma ya fuskanci hukunci.
Yayin da ake aika masa sammacin kira, Shugaban Kwamiti Amobi Ogah ɗan LP daga Abiya, ya ragargaji Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya, Kachollom, tare da cewa daga yanzu kwamitin ba zai lamunci rashin ladabi da biyayya daga kowane ma’aikatacin gwamnati ba.
“Daga yau ba za mu ƙara lamuntar rashin ladabi daga ma’aikacin gwamnati ba. Muna magana kan abin da ya shafi lafiyar ‘yan Najeriya. Za mu yi amfani da ƙarfin doka mu sa a kamo Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya idan ya ƙi halartar gayyatar da muka yi masa. Dalili kenan shi ma Ministan Lafiya ɗin muka gayyace shi, duk da cewa ba a zamanin sa aka ramto kuɗaɗen ba.”
Ogah ya ce dangane da waɗannan kuɗaɗe Dala miliyan 300, kwamiti ya samu kwafen takardun ƙorafe-ƙorafe ne daga Lauyoyin Seasons Law Firm, a madadin Rosies Textile Mills Limited, inda suka kawo ƙorafin cewa ma’aikatar lafiya ta ƙasa da Babban Sakataren ma’aikatar sun masu yin gidan sauro na cikin gida Najeriya shiga neman kwangilar samar da gidajen sauro da sauran ababen da suka danganci yaƙi da zazzaɓin cizon sauro.
Ya ce su na bincike ne domin sanin yadda aka kashe kuɗaɗen, shi ya sa suka gayyaci Babban Sakatare, amma ya ƙi halarta.
“Shin sun yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace ko kuwa? Idan ba su kashe kuɗaɗen ba, ina suka kai kuɗaɗen?
“Wannan fa tambaya ce mai sauƙi kuma mai buƙatar amsa mai sauƙi daga gare su. Amma sai noƙe-noƙe suke yi, mun kira su, sun ƙi bayyana, sai kiran manyan mutane daban-daban suke yi su na yi mana magana. Amma mu dai aikin mu shi ne mu kare haƙƙin ‘yan Najeriya, shi ya sa suka zaɓe mu.
“Ba za mu bari ‘yan Najeriya su ci gaba da mutawa ba, yayin da gwamnati a na ta ɓangaren ta yi ƙoƙarin ganin an kakkaɓe zazzaɓin maleriya nan da 2030.”
Discussion about this post