Sojojin Najeriya sun yi awon-gaba da basaraken masarautar Ewu, cikin Ƙaramar Hukumar Ighelli ta Kudu a Jihar Delta, bayan ya miƙa kan sa a hannun ‘yan sanda.
Basaraken mai suna Clement Ikolo dai sojoji ne suka ayyana cigiyar sa ruwa jallo tare da wasu mutum takwas da sojojin ke zargi suna da hannu a kisan-gillar soja 17 a ranar 14 Ga Maris a yankin Okuama.
PREMIUM TIMES ta ji cewa Ikolo ya kai kan sa hannun ‘yan sanda ne a jihar, a ranar Alhamis.
Sojojin Najeriya sun ɗauko Ikolo cancak a jirgin sojoji daga Delta zuwa Hedikwatar Sojojin Najeriya da ke Abuja, a ranar Juma’a.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Delta ta damƙa shi ga Sojojin Najeriya a ranar Juma’a, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka tabbatar.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Delta, Bright Edafe, bai amsa kiran da wakilin mu ya yi masa, kuma mai turo amsar saƙon tes da aka yi masa, domin ƙoƙarin jin ta bakin sa kafin a buga wannan labari.
An tabbatar da cewa wasu danƙara-danƙaran sojoji ne suka kai shi filin jirgin Delta, daga can jirgin kuma Air Peace ya ɗauke shi zuwa Abuja, wajen ƙarfe 9 na safe.
Discussion about this post