Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa a guiwa ba sai ta ga an ceto duka yaran makaranta da ƴanbindiga suka sace a Kaduna ranar Alhamis.
Idan ba a manta ba ƴanTadda sun sace yaran makarantan Firamare sama da 100 a garin Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ranar Alhamis.
Gwamna Sani ya kai ziyara garin Kuriga inda ya sha alwashin cewa gwamnati za ta ceto duka yaran nan ba da dadewa ba.
” Ku yi hakuri, tunda abin nan ya faru ban samu sukuni ba, ina tabbatar muku cewa nan ba da dadewa ba za a ceto yaran dukkan su.
” Na yi magana da shugaban kasa sannan na yi magana da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu kuma duk za a tabbatar an ceto yaran nan.
Discussion about this post