Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce wasu daga cikin rahotannin sace-sacen jama’a da ake yi a Abuja shirya su ake yi kawai da yawa ba da gaske ƴanta’addan bane.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba jim kadan bayan ya yi wata ganawar sirri da majalisar dattawa a ranar Laraba.
Wike ya bayyana a gaban ƴanmajalisar ne tare da kwamishinan ƴansanda na babban birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh, domin tattaunawa kan yadda ake samun karuwar masu garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro a Abuja.
Wike ya shaidawa manema labarai cewa an shirya wasu daga cikin abubuwan da suka faru na garkuwa da mutane.
“Wasu daga cikin labaran sace-sacen da kuke ji mutane ne ke shirya su, akwai wasu a cikin gida a ke tsara yadda za a yi garkuwar don a karɓi kuɗin fansa.
“Misali, za ku ga da ma’aikacin gida ko direba a gidan ake shirya makarkashiyar sace yaron mai gida, irin haka ya ya mu za mu yi, iyakan mu tabbatar an ceto wanda aka sace cikin koshin lafiya.
Ministan ya jaddada cewa sace-sacen mutane a Abuja ya ragu matuka, saboda kara ƙaimi da jami’an tsaro suka yi wajen kakkaɓe ayyukan ƴanTa’adda a Abuja.
Discussion about this post