A taron Majalisar Zartaswa ta Jihar Jigawa na ranar Litinin, 25 ga Maris, 2024, an amince da ƙudurori kamar haka:
Majalisar Zartaswa ta duba Rahoton Kwamitin Tantance Rahoton Kwamitin Bincike a kan Manyan Makarantun Koyar da Ayyukan Kiwon Lafiya na jiha, inda ta umarci Ofishin Babban Akanta na jiha da ya aiwatar da shawarwarin da wannan kwamiti ya bayar tare da ɗaukar waɗannan matakai:
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Namadi ya fitar a shafin sa na Facebook, ya ce mataki na farko shi ne sauke Shugabannin Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Birnin Kudu da suka haɗa da Shugaban Kwaleji, Babban Jami’in Kula da Kuɗaɗe da Rajistara, tare da umarnin su kai kan su Ma’aikatar Lafiya, Ofishin Shugaban Ma’aikata da Babban Akanta.
Sannan kuma an sauke daraktocin Makarantun Koyon Aikin Jinya na Birnin Kudu, Hadejia da Babura daga muƙaman su, kuma za su kai kan su Ma’aikatar Lafiya.
“Daraktocin makarantun a Birnin Kudu, Hadejia da Babura za su biya kuɗaɗen da suka kasa bayar da ba’asi a kan su.
An sauke ‘Provost’, ‘Bursar’ da ‘Registrar’ na Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun daga muƙaman su sannan kuma za su kai kan su Ma’aikatar Lafiya, Ofishin Shugaban Ma’aikata da Babban Akanta.
‘Provost’ na Kwalejin Kiwon Lafiya zai bayar da dalilai kan ɓacewar kuɗaɗen shiga na kwalejin da waɗanda aka samu daga gwamnati waɗanda ba a bayar da ba’asins u ba.
Dukkan jami’an da suke karɓar albashin da bai kamata su karɓa ba sannan kuma ba a makarantun suke aiki ba amma sunayen su suke kan jadawalin albashi na makarantun, za su mayar da kuɗaɗenn da suka karɓa wanda ba haƙƙin su ba ne.
Ma’aikatar Lafiya za ta sabunta gine-gine da kayan aiki a Makarantun Koyon Aikin Jinya na Birnin Kudu, Hadejia da Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun.
Ma’aikatar Lafiya za ta ɗauki ƙarin ma’aikata domin cike giɓin ƙarancin malamai a waɗannan makarantu biyu.
Gwamnati za ta kafa Hukumomin Gudanarwa na waɗannan makarantu biyu.
Ma’aikatar Lafiya za ta ƙara kuɗin abinci na ɗaliban Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jahun.”
Discussion about this post